Candido ya ce zai ba marada kunya

dan takarar Shugaban karamar Hukumar Birnin Abuja (AMAC) a karkashin Jam’iyyar APC, Alhaji Abdullahi Adamu Candido ya ce zai jajirce domin ganin ya ba marada kunya in aka zabe shi a matsayin shugaban karamar hukumar a zabe mai zuwa.Abdullahi Candido ya fadi hake ne a lokacin da ya je yakin neman zabe a kyauyen Karmajiji […]

Candido ya ce zai ba marada kunya
Candido ya ce zai ba marada kunya

dan takarar Shugaban karamar Hukumar Birnin Abuja (AMAC) a karkashin Jam’iyyar APC, Alhaji Abdullahi Adamu Candido ya ce zai jajirce domin ganin ya ba marada kunya in aka zabe shi a matsayin shugaban karamar hukumar a zabe mai zuwa.
Abdullahi Candido ya fadi hake ne a lokacin da ya je yakin neman zabe a kyauyen Karmajiji da ke kan titin Filin Jirgin Sama na Abuja inda ya ce lokaci ya yi da za a tallafa wa ma’aikata wadanda suke aikin gina kasa kuma suke zaune a kwaryar birnin Abuja, inda ya ce ya kamata su ma a sama musu ababen jin dadin rayuwa.
Alhaji Abdullahi Candido ya ce ya ziyarci kungiyar hadin kai da ci gaban Hausawa mazauna Karmajiji ne don nuna cewa duk dan Najeriya yana da gudunmawar da zai bayar wajen gina kasa, inda ya ce sai da zaman lafiya ne ake samun ci gaba.
Ya ce manufar Jam’iyyar APC ita ce ta kawo sauyi domin a gina kasa ba a bar mutane kadan suna handama da babakere ba.
A jawabin Shugaban Hausawa mazauna Karmajiji, Alhaji Aminu Alkali ya ce manufar kafa kungiyar ita ce domin a taimaka wa juna tare da bin doka da oda.