Canja hukuncin shekara bakwai a gidan yari maimakon rai-da-rai ga masu safarar mutane a Najeriya ya dace?

A can baya, ga duk mutumin da aka kama da laifin safarar mutane a Najeriya, hukuncin daurin rai-da-rai ake zartar masa, amma a yanzu an canja hukuncin da daurin shekara bakwai a gidan yari. Abin tambaya a nan shi ne, shin wannan canji ya dace ko bai dace ba? Ga abin da mutane suka bayyana, […]

Canja hukuncin shekara bakwai a gidan yari maimakon rai-da-rai ga masu safarar mutane a Najeriya ya dace?
Canja hukuncin shekara bakwai a gidan yari maimakon rai-da-rai ga masu safarar mutane a Najeriya ya dace?

A can baya, ga duk mutumin da aka kama da laifin safarar mutane a Najeriya, hukuncin daurin rai-da-rai ake zartar masa, amma a yanzu an canja hukuncin da daurin shekara bakwai a gidan yari. Abin tambaya a nan shi ne, shin wannan canji ya dace ko bai dace ba? Ga abin da mutane suka bayyana, kamar yadda wakilanmu suka kalato mana:

Canjin ya dace – Auwalu Laleko

Alhaji Auwal Laleko: “Ni wana ra’ayin, daurin shekara bakwai ya fi dacewa ga masu wannan harka ba daurin rai-da-rai ba. Duk irin laifin da mutum  ya yi, akwai hukuncin da ya dace a yi masa daidai laifinsa ba a daukar laifi kamar wanda ba za a yafe ba. Idan mutum yana wannan harka aka kama shi aka yi masa dauri na wasu shekaru, idan ya fito ana sa ran zai canja halinsa amma idan hukuncin ya yi tsanani; yaushe ake tsammanin mutumin nan zai gyaru bayan kuma duk wani laifi akan iya sassauci a kansa? Ni ba na goyon bayan masu safarar yara amma dai su ma wadanda suka sassauta hukuncin sun yi tunani ne a kai sannan suka rage. Don haka jama’a su dubi lamarin da ido mai kyau.”