Canja hukuncin shekara bakwai a gidan yari maimakon rai-da-rai ga masu safarar mutane a Najeriya ya dace? 1

A can baya, ga duk mutumin da aka kama da laifin safarar mutane a Najeriya, hukuncin daurin rai-da-rai ake zartar masa, amma a yanzu an canja hukuncin da daurin shekara bakwai a gidan yari. Abin tambaya a nan shi ne, shin wannan canji ya dace ko bai dace ba? Ga abin da mutane suka bayyana, […]

Canja hukuncin shekara bakwai a gidan yari maimakon rai-da-rai ga masu safarar mutane a Najeriya ya dace? 1
Canja hukuncin shekara bakwai a gidan yari maimakon rai-da-rai ga masu safarar mutane a Najeriya ya dace? 1

A can baya, ga duk mutumin da aka kama da laifin safarar mutane a Najeriya, hukuncin daurin rai-da-rai ake zartar masa, amma a yanzu an canja hukuncin da daurin shekara bakwai a gidan yari. Abin tambaya a nan shi ne, shin wannan canji ya dace ko bai dace ba? Ga abin da mutane suka bayyana, kamar yadda wakilanmu suka kalato mana:

Canja hukuncin bai dace ba – Abubakar Babayo

Abubakar Babayo: “Ni a nawa ra’ayin, a daure wanda yake sana’ar safarar yara rai-da-rai shi ya fi kamata, ba shekara bakwai kamar yadda majalisa ta amince a kai ba. A gani na, duk wadanda suka goyi bayan a dawo da wannan hukunci shekara bakwai ba na rai-da-rai ba, ina ganin kamar su ne iyayen gidan masu wannan harka ta safarar yara, domin duk wanda zai yi safarar dan wani idan ka taba nasa ba zai ji dadi ba; to don me zai yi safarar ’ya’yan wasu, su ba ’ya’ya ba ne? Duk wanda yake wannan harka kuma ya san ba ta da kyau, idan aka kama shi za a yi masa daurin shekara bakwai, yana sa ran zai fita gaba kuma zai ci gaba amma idan yasan daurin da za a yi masa na rai-da-rai ne; ba zai yarda ya shiga wannan harka ba kuma hakan zai zama darasi ga na baya.”