Canja hukuncin shekara bakwai a gidan yari maimakon rai-da-rai ga masu safarar mutane a Najeriya ya dace? 2

A can baya, ga duk mutumin da aka kama da laifin safarar mutane a Najeriya, hukuncin daurin rai-da-rai ake zartar masa, amma a yanzu an canja hukuncin da daurin shekara bakwai a gidan yari. Abin tambaya a nan shi ne, shin wannan canji ya dace ko bai dace ba? Ga abin da mutane suka bayyana, […]

Canja hukuncin shekara bakwai a gidan yari maimakon rai-da-rai ga masu safarar mutane a Najeriya ya dace? 2
Canja hukuncin shekara bakwai a gidan yari maimakon rai-da-rai ga masu safarar mutane a Najeriya ya dace? 2

A can baya, ga duk mutumin da aka kama da laifin safarar mutane a Najeriya, hukuncin daurin rai-da-rai ake zartar masa, amma a yanzu an canja hukuncin da daurin shekara bakwai a gidan yari. Abin tambaya a nan shi ne, shin wannan canji ya dace ko bai dace ba? Ga abin da mutane suka bayyana, kamar yadda wakilanmu suka kalato mana:

Kwaskwarimar hukuncin ba ta dace ba – Bello Tangaza

Bello Tangaza: “Ni ban goyi bayan wannan kwaskwarima ba. Dalilina kuwa kan wannan shi ne, ta’addanci zai yi yawa domin mutane ba su tsoron hukuncin da ke da wa’adin karewa. Bai ko kamata a sassauta ba in har ba a kara tsananta musu ba. Sassauta dokar shi ke kawo wadansu su aikata laifin. A nawa ra’ayin, duk wanda ya aikata laifin, kisa kawai ya dace da shi domin daidai yake da dan fashi da makami. Masu aikata wannan mummunar dabi’a sukan yi kisa a wasu lokuta. Irin wannan lamarin ya taba faruwa a nan Sakkwato a ’yan kwanakin da suka gabata, masu wannan shegiyar dabi’a suka bata zuri’ar da suka aikata wa wannan aika-aikar, har ka ga al’umma sun ki wadda musibar ta fada mawa, sai kaga rayuwa ta rushe gaba daya.”