Canja hukuncin shekara bakwai a gidan yari maimakon rai-da-rai ga masu safarar mutane a Najeriya ya dace? 3
A can baya, ga duk mutumin da aka kama da laifin safarar mutane a Najeriya, hukuncin daurin rai-da-rai ake zartar masa, amma a yanzu an canja hukuncin da daurin shekara bakwai a gidan yari. Abin tambaya a nan shi ne, shin wannan canji ya dace ko bai dace ba? Ga abin da mutane suka bayyana, […]
A can baya, ga duk mutumin da aka kama da laifin safarar mutane a Najeriya, hukuncin daurin rai-da-rai ake zartar masa, amma a yanzu an canja hukuncin da daurin shekara bakwai a gidan yari. Abin tambaya a nan shi ne, shin wannan canji ya dace ko bai dace ba? Ga abin da mutane suka bayyana, kamar yadda wakilanmu suka kalato mana:
Kwaskwarimar hukuncin ta yi daidai amma… – Mahmud Mahmud
Mahmud Mahmud: “Ita gaskiya fa daya ce kuma da zaran an kuskure mata sai bata. Don haka nake ganin ya dace a yi wa hukuncin kwaskwarima amma ba wai a mayar da shi shekara bakwai ba, sai dai aiki mai tsanani kafin kashewa, wannan zai sa kowa ya tsorata amma an ce shekara bakwai ai mutum zai dauki ba wani abu ba ne kai da ma a bar shi daurin-rai-da rai da a zo mana da wannan sabon hukunci da yawa mutane in aka ce masu za su ida rayuwarsu a gidan maza ba sa so, don sun san dusa ce da manja za su rika ci. Ka ga wahala za ji masu ke nan. Magana ta adalci, ya kamata hukuma ta kula wannan laifin ba karami ba ne da ake kokarin sassautawa saboda haka a farga, kada irin halin da Indiya da sauran kasashe suka shiga mu ma su same mu. Don haka a yi kwaskwarima amma ba shekara bakwai ba.”