Canja hukuncin shekara bakwai a gidan yari maimakon rai-da-rai ga masu safarar mutane a Najeriya ya dace? 4
A can baya, ga duk mutumin da aka kama da laifin safarar mutane a Najeriya, hukuncin daurin rai-da-rai ake zartar masa, amma a yanzu an canja hukuncin da daurin shekara bakwai a gidan yari. Abin tambaya a nan shi ne, shin wannan canji ya dace ko bai dace ba? Ga abin da mutane suka bayyana, […]
A can baya, ga duk mutumin da aka kama da laifin safarar mutane a Najeriya, hukuncin daurin rai-da-rai ake zartar masa, amma a yanzu an canja hukuncin da daurin shekara bakwai a gidan yari. Abin tambaya a nan shi ne, shin wannan canji ya dace ko bai dace ba? Ga abin da mutane suka bayyana, kamar yadda wakilanmu suka kalato mana:
Sassaucin hukuncin bai dace ba – AbubakarGarba
Abubakar Garba Usman: “A gaskiya ba daidai ba ne a yi sassaucin hukumci irin wannan ga masu safarar mutane ba. Kamata ya yi a bar hukuncin daurin rai-da-rai ko kuma ya zama hukuncin kisa. Hukumci mai tsanani ne ya dace da irin wadannan mutane, domin zai sa masu sha’awar yin hakan su tsorata. Hukuncin shekara bakwai ga masu safarar mutane ya yi kadan kwarai da gaske.”