Canja hukuncin shekara bakwai a gidan yari maimakon rai-da-rai ga masu safarar mutane a Najeriya ya dace? 5
A can baya, ga duk mutumin da aka kama da laifin safarar mutane a Najeriya, hukuncin daurin rai-da-rai ake zartar masa, amma a yanzu an canja hukuncin da daurin shekara bakwai a gidan yari. Abin tambaya a nan shi ne, shin wannan canji ya dace ko bai dace ba? Ga abin da mutane suka bayyana, […]
A can baya, ga duk mutumin da aka kama da laifin safarar mutane a Najeriya, hukuncin daurin rai-da-rai ake zartar masa, amma a yanzu an canja hukuncin da daurin shekara bakwai a gidan yari. Abin tambaya a nan shi ne, shin wannan canji ya dace ko bai dace ba? Ga abin da mutane suka bayyana, kamar yadda wakilanmu suka kalato mana:
daurin-rai-da-rai ya fi dacewa– Babangida ’Yankara
Alhaji Babangida Yankara: “Ya kamata a bar hukuncin yadda yake, bai kamata a rage ba. Irin wadannan mutane su ne suka yi sanadin mutuwar Sarkin Musulmi kuma sun yi nasarar sace mutane masu dangantaka da manyan mutane. To, idan ba a yi musu hukumci mai tsanani ba ai ka ga ke nan ana karfafa musu gwiwar ci gaba da aikata wannan ta’asa, wacce babu wanda ya san wadanda za su dirarwa a nan gaba.”