Canja Sheka: Aledis Sanches zai koma Inter Milan
Rahotanni daga kulob din Manchester United na Ingila sun ce a shekaranjiya Laraba, kulob din ya kulla yarjejeniya da Inter Milan da ke Italiya game da bayar da aron dan kwallonsa Aledis Sanchez. Kungiyoyin biyu sun amince Sanchez ya koma Inter Milan ne a matsayin aro. Sai dai Inter Milan ta ki amincewa ta biyan […]
Alexis Sanchez
Rahotanni daga kulob din Manchester United na Ingila sun ce a shekaranjiya Laraba, kulob din ya kulla yarjejeniya da Inter Milan da ke Italiya game da bayar da aron dan kwallonsa Aledis Sanchez.
Kungiyoyin biyu sun amince Sanchez ya koma Inter Milan ne a matsayin aro. Sai dai Inter Milan ta ki amincewa ta biyan Sanchez albashin Fam dubu 400 a mako (kimanin Naira biliyan 1 da miliyan 768), inda ta nemi a rage zuwa Fam dubu 150 ((kimanin Naira miliyan 663) a mako.
Idan yarjejeniyar ta tabbata Sanchez zai koma Inter ne kafin ranar Litinin mai zuwa ranar da za a rufe cinikin ’yan kwallo a Nahiyar Turai.
A watan Janairun bara ne Sanchez ya canja sheka daga Arsenal zuwa United. Kuma ya yi wasanni 45 inda ya zura kwallaye biyar kacal a raga.
Tun bayan da aka fara kaka ta bana Sancez bai yi wa United wasa ko daya ba.
Idan Sanchez ya koma Inter Milan zai hadu da takwaransa Romelu Lukaku da suka yi kwallo tare a United wanda shi ma ya canja sheka zuwa can.