Canji da Buhari: Abin baina – baina ne (2)
Tijjani Salisu Ahlan:Abin mamaki shi ne ka kashe wuta, kuma hayaki ya kore ka! Na tabbata jajircewa a kawar da waccan gwamnatin ya fi wahala da radadi a kan wannan tsawwalar farashin. Na tabbata firgici da rashin tabbas da muka samu kanmu a ciki a baya, ya fi wannan karancin abubuwan amfani. Kuma ya kamata […]
Tijjani Salisu Ahlan:
Abin mamaki shi ne ka kashe wuta, kuma hayaki ya kore ka! Na tabbata jajircewa a kawar da waccan gwamnatin ya fi wahala da radadi a kan wannan tsawwalar farashin. Na tabbata firgici da rashin tabbas da muka samu kanmu a ciki a baya, ya fi wannan karancin abubuwan amfani. Kuma ya kamata mu lura, idan mun ce muna jin wahala a yanzu, to ke nan mun fito ne can daga jin dadi ne?
A’a, dama a wahalar muke, kuma ta banza. Tunda babu wani alheri da muke zato, amma matsalarmu ta yanzu ai muna da kyakkyawan zaton gushewarta.
Kuma a yanzu kowa yana jin wahalar ne tsakanin mu talakawan da shugabannin da attajiran kasar, wannan kuwa alama ce da ke nuna lallai gyara yana kyau. Ka dubi yadda ’yan majalisa ke jajen kudi sun yi musu kadan, dubi yadda ’yan kasuwa ke taka-tsantsan. Don haka mu daure yau da gobe ce…
Abdulmumin Yakub:
Allah Ya gafarta. Mu fa a Najeriya duk inda muke ta hanya biyu ake gane mu (mafi yawanci), don ni a nawa tunanin ko dai a jini ne ko halitta ne abin. Allah Ya albarkaci dan Najeriya da rashin hakuri, haka kuma wannan kan jawo halin ko in kula da kin gaskiya. Allah Ya sa wa dan Najeriya kabilanci da kin gaskiya, sannan da halayyar nan ta ko in kula, ko idan ba da ni ba, to kowa ma ya rasa. Ka dubi barayin zaune da na biro duk ba sa da laifi ga wasu ’yan Najeriya, amma Buhari da ya tono su shi ne mai laifi. Allah Ya taimaki Buhari a kan kudirinsa ga Najeriya da mu ’yan Najeriya.
Dangane da matsalar Boko Haram da tsadar kayan masarufi kuwa, duk mai adawa a kan wannan to ya ba kansa amsa a kan wannan tambaya. Shin da tashin bam da tashin Dala wanne ya fi kai a wajenka? Haka kuma idan muka yi dubi a rayuwa, hadari ko ciwo su ke kama mutum nan take, amma sauki sannu a hankali yake samuwa.
Abdulkadir Badamasi:
bata gari suna aiki tukuru don ganin sun bata Buhari a idon jama’a, wadancan tsofaffin gafiyoyin sun baza kananan beraye a kowane sako da lungun kasar nan da niyyar gamsar da talakawa wai bara ta fi bana. Shi kuma talaka bawan Allah, bai san gafiyoyi da beraye sun gama bata komai ba, sun sace arzikin kasar kuma sun kashe duk wata hanya ta samun arzikin. To zuwan canji sai suka ga idan fa aka samu tabbatar canjin nan asirinsu zai tonu, ta’asar da suka tafka za ta fito fili, don haka suke duk wani kokari na kawo cikas ga wannan gwamnati. Amma sun makara idan ana samun rubuce-rubuce irin wadannan a yanar gizo da jaridu, kuma ana kokarin wayar da kan jama’a, to ba za su yi nasara ba, kuma canji zai tabbata. Allah Ya saka da alheri
Abubakar Babayaro:
Allah Sarki! Ai jama’a har yanzu sun gaza gane shugaba nagari da kuma dan kasa nagari, wato tsakanin dan kasa nagari da kuma mutum nagari, misali kamar a Kaduna tsakanin Malam Nasiru da Mukhtar, haka kuma kamar mai kudi da mai arziki. Na zayyyana da halayyarsu sai mu dan kwatanta su da rayuwar Bahari da kuma na wani a kasar da ake ganin cewa ana iya kwatanta shi da Baharin. A karshe ina cewa Bahari mutum ne nagari kuma dan kasa nagari, wanda kuma za a gama shi da Buhari sai mu ga yadda zai kasance!
Umar Sidi Ahmad:
Gaskiya muna da matsala babba, ga gaggawa, ga son kai, ga rashin adalci. Mafiya yawa daga cikinmu muna son ganin Shugaba Buhari ya gyara komai cikin kankanen lokaci kamar zai ce wa lamurra, (KUN FA YA KUNU). Mu tuna da irin wahalhalun da Buhari yake sha, yau yana nan, jiya ya je can, gobe ma zai je can duk don ganin ya sama wa kasarmu da mu kanmu mafita. Allah Ya ba shi ikon samun nasara wurin gyarawa, mu kuma ya ba mu ikon hakuri da fahimtar al’amura.
Muhammad Salis Jibril:
Wani abin takaicin ma shi ne, mutanen Arewa (yankin da Shugaba Buhari ya fito) su ne suka fi kowa kwarmato da kwakwazo da mugun alkaba’i ga wannan gwamnati. Kodayake, ban yi mamaki ba domin marigayi Malam Sa’adu Zungur ya fadi wasu kalamai game da al’ummar Arewa a cikin wakarsa yana cewa:
A Arewa zumunta ta mutu,
Sai nishadi sai sharholiya.
Sai alfahari da yawan kwafe,
Girman kai sai kwambon tsiya.
Camfe-camfe da tsibbace-tsibbacen,
Malaman karya ’yan duniya.
Babu mai aiki bisa hankali,
Da basira don ya ga gaskiya.
Rantse-rantse da Allah yai yawa,
Ga karya ga zambar tsiya.
Gorin asali da na dukiya,
Sai ka ce dan “Annabi Fariya.”
Sai kinibibi, sai kwarmato,
Ga gulma da son kullalliya.
Murtala Sirajo:
Maganar gaskiya ba ba mu ganin kokarin shi Buhari ba ne ba, a’a, abubuwan ne sun tsananta da yawa kuma kullum kara tsananta suke, misali matsalar mai an sha yin ta a baya, amma ba a taba wuyar mai tare da tsadarsa irin wannan lokaci ba. Ni a tunanina idan gyara za a yi me zai hana a rike mutane a kan yadda suke, ba tare da an galabaitar da su ba, sai a ci gaba da aikin samar musu da sauki suna a halin da suka saba da saukin ya samu sai a dauke su daga nan a maida su wurin sauki, ina ga kamar haka zai fi.
Abdulkareem Raubilu:
Ni a dan karamin tunani da nazarina sai in ga maganar uzuri ba hujja ba ce, saboda shi wanda ake cewa a yi wa uzurin ya yi biris da ko-in-kula da halinn kunci da damuwa da talaka yake ciki. A tuna fa kafin ya hau mulkin abin da yake nunawa shi zai yi don talaka ne, kuma talakawa suka aminta da shi, suka tsaya kai da fata sai shi din. Amma abin takaici shi ne ya hau din amma sai wahala da tsanani, babu ta dadu fiye da yadda ake da, kuma har yanzun shiru kake ji ba wani alamun an kamo hanyar samar da saukin. Tambayata ita ce wai kuna ganin idan shi ne yake cikin halin da talakawan nan suke, zai shiru ba zai yi korafi ba? Wallahi na san ba zai yi shiru ba. Domin a lokacin kamfen dinsa ya fake ne da cewa kasar tana cikin wani hali idan ba a ba shi kuri’a ya ceto ta ba, za ta shiga mawuyacin hali. Sai ga shi, shi da aka tura don ceto ya zama dan cuta. Don haka don Allah mu cire maganar uzuri a nan, domin muna cutar kanmu da shi ne kawai, mu fito mu fada masa gaskiar al’amari ko zai gyara, domin idan ba zai iya gyaran ba, ya sauka ya bar mu a yadda muke.
Mun kammala