Canjin Kudi: APC ta nemi Emefiele da Malami su yi murabus

Mataimakin Shugaban APC na Yankin Arewa maso Yamma, ya nemi su ajiye mukamansu saboda rudin da suka yi wa Shugaba Muhammadu Buhari

.

Canjin Kudi: APC ta nemi Emefiele da Malami su yi murabus

Jam’iyyar APC ta bukaci Ministan Shari’a Abubar Malami tare da Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, su ajiye mukamansu saboda rudin da suka yi wa Shugaba Muhammadu Buhari wajen kafa dokar sauyin kudi.

Mataimakin Shugaban APC na Yankin Arewa maso Yamma, Salihu Mohammed Lukman, ne ya yi wannan kira a ranar Juma’a, jim kadan bayan Kotun Koli ya ayyana dokar haramta amfani da tsoffin takardun kudi na N200 da N500 da kuma N1,000 a matsayin haramtacce.

A tsokacinsa kan hukuncin Kotun Kolinsa, ya ce “A kasashen da dimokuradiyya ta kafu sosai, duk jami’in gwamnati ta ya saba doka irin haka, ajiye mukaminsa yake yi.

“Tunda ya tababta cewa sauyin kudin ta saba wa dokokin Najeriya, ya kamata Emefiele da Malami su amince suna da karancin fahimtar doka da tsarin dimokuradiyya, su yi murabus nan take.”

Ya ci gaba da cewa, “Abin takaici ne yadda aka rudi Shugaba Buhari ya aika wannan abin da Kotun Koli ta bayyana cewa saba doka ne da kuma amfani da karfin iko ta hanyar da bai dace ba.

“Bisa la’akari da irin illar da zuwa yanzu dokar takaita amfani da tsabar kudi, wadda Kotun Koli ta ce haramtacce ne, da kuma yadda hakan ya taba kimar Shugaba Buhari, ya kamata Emefile da Malami, su dauki laifin duk abin da ya faru.”

A ranar Juma’a ce kwamitin alkalai bakwai na Kotun Koli suka yi watsi da dokar sauyin kudin, wadda ta jefa miliyoyin ’yan Najeriya cikin kuncin rayuwa, kuma duk da cewa sun nuna adawarsu da lamarin, Gwamnatin Tarayya ta ki janye dokar.

Gwamnatocin jihohin Kaduna, Kogi da Zamfara ne dai suka fara maka Gwamnatin Tarayya a Kotun Koli suna neman ta dage wa’adin amfani da dokar saboda abin da suka kira wahalar da ta jefa talakawa.

Daga bisani wasu jihohi 16 suka bi sahunsu a gaban kotun.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya