Canjin kudi dabara ce ta tunzura ’yan Najeriya su zabi Atiku – Sanatan APC

Sai dai ya ce yanzu kan ‘yan Najeriya ya waye

Canjin kudi dabara ce ta tunzura ’yan Najeriya su zabi Atiku – Sanatan APC

Smart Adeyemi

Sanata mai wakiltar mazabar Kogi ta Yamma a Majalisar Dattijai, Smart Adeyemi, ya bayyana canjin kudi a matsayin wani yunkuri na ganin bayan dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu.

Da yake zantawa da manema labarai a sakatariyar APC da ke Abuja ranar Litini, Sanatan ya kuma yi zargin cewa da gangan aka kirkiro manufar da nufin fusata ’yan Najeriya su zabi dan takarar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar.

Sai dan majalisar ya ce a yanzu kan ’yan Najeriya ya waye, ba za su sake yarda da masu kokarin yi wa Dimokuradiyya zagon kasa ba.

Smart Adeyemi ya ce, “Da gangan aka kirkiri wannan shirin don share wa dan takarar PDP fage, amma yanzu ’yan Najeriya sun waye. Me ya sa kuke tunanin jam’iyya mai mulki za ta fito da irin wannan manufar da za ta kuntata wa mutanen da take neman kuri’arsu?

“Sun kawo wannan batu ne na canjin kudi domin su shafa wa Tinubu kashin kaji. Tinubu yana kirkirar arziki, Atiku kuma yana sayar da shi. Shi kuwa Peter Obi tausayinsa nake ji saboda hangen Dala yake yi wa siyasa.

“Me zai sa mu zabi Atiku? Ba shi ya jagoranci cefanar da kadarorin gwamnati ga rubabbun kamfanoni a baya ba? Duk wadanda ba su san tarihi ba ne suke ta ihun sai Atiku. Atiku ba shi ne mafita ba ga Najeriya.

“Gwamnonin Arewa sun tsaya kai da fata cewa sai mulki ya koma Kudu, kuma tarihi zai tuna da su a kan wannan sadaukarwar. Wannan zabe ne tsakanin Tinubu da Peter Obi.

“Jiya-jiyan [Lahadi] nan ilahirin shugabannin jam’iyyar LP na shiyyar Arewa maso Yamma suka narke suka koma tafiyar APC. To ta yaya Obi zai ci wannan zaben? Tabbas sai dai ya tara a wani jikon, amma ba wannan ba,” in ji Sanatan na APC.