Canjin Kudi: Gwamnonin APC sun bukaci Buhari ya bi umarnin Kotun Koli

Gwamnonin APC da Shugaban Jam’iyyar, Abdullahi Adamu, sun bukaci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) da Atoni-Janar na Kasa su yi biyayya ga umarnin Kotun Koli na dakatar da aiwatar da dokar sauya kudi. Shugaban jam’iyyar ne ya bayyana hakan ga manema labarai bayan kammala taronsa da gwamnonin a sakatariyar jam’iyyar […]

Canjin Kudi: Gwamnonin APC sun bukaci Buhari ya bi umarnin Kotun Koli

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu

Gwamnonin APC da Shugaban Jam’iyyar, Abdullahi Adamu, sun bukaci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) da Atoni-Janar na Kasa su yi biyayya ga umarnin Kotun Koli na dakatar da aiwatar da dokar sauya kudi.

Shugaban jam’iyyar ne ya bayyana hakan ga manema labarai bayan kammala taronsa da gwamnonin a sakatariyar jam’iyyar da ke Abuja.

Adamu ya ce kasancewar dokar na wahalar da ’yan Najeriya, ya zamo dole Gwamnati ta yi biyayya ga kotun koli.

“Kin yi wa Kotun Koli biyayya na jawo asara ga tattalin arzikin Najeriya, don haka muna kira da babbar murya ga Atoni-Janar na Kasa da Gwamnan CBN, da su yi biyayya ga umarnin Kotun Koli.

“Muba kuma kira ga shugaban kasa da ya shiga lamarin, don talakawa na wahala, tattalin arzikin Najeriya kuma na raunana.

Shi ma dai Gwamnan Jihar Kebbi, kuma Shugaban Kungiyar Gwamnonin APC, Atiku Bagudu, ya ce matsayarsu daya da shugaban jam’iyyar.

“Daga shugaban jam’iyya har gwamnoni matsayar mu ke nan.”

Bayan fara taron da sa’o’i biyu dai an hango dan takarar shugaban kasar APC Bola Tinubu ya shiga fagen, sai dai bai tsaya ganawa da manema labarai ba.

Haka kuma har ya ta tafi bayan taron bai ce wa ’yan jarida uffan ba.