Canjin Naira 100 ya janyo salwantar ran mutum biyu a Legas

Wani lamari mai tada hankali wanda ya samo asali daga batun canjin Naira 100 ya yi sanadiyar salwantar ran mutum biyu fasinja da yaron mota a Legas. Lamarin wanda ya dauki hankalin al’ummar yankin, wata majiya da ta shaidi faruwar lamarin ta ce wani fasinja ne ya nemi yaron motar ya ba shi canjinsa Naira […]

Canjin Naira 100 ya janyo salwantar ran mutum biyu a Legas

Wani lamari mai tada hankali wanda ya samo asali daga batun canjin Naira 100 ya yi sanadiyar salwantar ran mutum biyu fasinja da yaron mota a Legas.

Lamarin wanda ya dauki hankalin al’ummar yankin, wata majiya da ta shaidi faruwar lamarin ta ce wani fasinja ne ya nemi yaron motar ya ba shi canjinsa Naira 100 lokacin da motar ta tsaya a inda zai sauka a yankin Kasuwar Asuwani da ke Isolo, inda nan take takaddama ta barke a tsakaninsa da yaron motar, sai yaron motar ya dauki wuka ya daba masa nan take ya mutu. Majiyar ta ce ganin haka sai wadansu matasa da ke kusa da suka rike yaron motar inda suka sanya masa taya suka cinna masa wuta ya kone kurmus suka kuma kone motar yayin da direbanta ya gudu don tsira da ransa.

Da Aminiya ta tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Legas, Chita Oti kan lamarin amma bai daga waya ba bai kuma ba da amsar sakon da aka aika masa ba.

A na samun yawan waitar daukar doka a hannu a baya-bayan nan a Jihar Legas inda mutane kan zartar da doka a kan duk wanda suke ganin ya aikata laifi, kuma a irin haka ne a mako biyu da suka shude wadansu matasa suka hallaka wani dan sanda bayan ya harbe jami’in hukumar kula da ababen hawa ta Jihar Legas.

Irin wannan daukar doka a hannu ta hanyar kisa tare kone gawa ba bakon abu ba ne a Jihar Legas sai dai an samu saukin lamarin bayan zuwan mulkin farar hula.