Canjin sheka a tsakanin ’yan siyasar kasar nan alheri ne ga dimokuradiyya? 2
Yadda canjin sheka ya zama ruwan dare a tsakanin ‘yan siyasar kasar nan ta sa wakilanmu suka bazama don jin ra’ayoyin jama’a a kan haka. Ga ra’ayoyin kowane daga ciki kamar haka Zai iya haifar da alheri a siyasar Najeriya – Abdullahi Alkwatonawi Abdllahi Alkwatonawi, “Duk da yake ba yau ‘yan siyasar Najeriya suka […]
Yadda canjin sheka ya zama ruwan dare a tsakanin ‘yan siyasar kasar nan ta sa wakilanmu suka bazama don jin ra’ayoyin jama’a a kan haka. Ga ra’ayoyin kowane daga ciki kamar haka
Zai iya haifar da alheri a siyasar Najeriya – Abdullahi Alkwatonawi
Abdllahi Alkwatonawi, “Duk da yake ba yau ‘yan siyasar Najeriya suka fara canja sheka daga wannan jam’iya zuwa waccan ba, amma ina ganin yin hakan yana da kyau kwarai kuma zai iya haifar da alheri ga irin siyasar dimukuradiyya da ake yi a kasar nan. Sannan kuma, zai yi amfani ga jama’a musamman su ‘yan siyasa da talakawa da za su iya koyon darasi na irin rayuwar da ta dace musu a cikin siyasa ta fannin gano mutanen kirki masu kishin al’umma da baragurbin da suke canja sheka domin aljihunsu.”