Canjin sheka a tsakanin ’yan siyasar kasar nan alheri ne ga dimokuradiyya? 3
Yadda canjin sheka ya zama ruwan dare a tsakanin ‘yan siyasar kasar nan ta sa wakilanmu suka bazama don jin ra’ayoyin jama’a a kan haka. Ga ra’ayoyin kowane daga ciki kamar haka Idan don ceton kasa suke yi alheri ne – Alhaji Muhammed Khalid Kwantagora Alhaji Muhammed Khalid Kwantagora, “Idan ‘yan siyasa suna ficewa daga […]
Yadda canjin sheka ya zama ruwan dare a tsakanin ‘yan siyasar kasar nan ta sa wakilanmu suka bazama don jin ra’ayoyin jama’a a kan haka. Ga ra’ayoyin kowane daga ciki kamar haka
Idan don ceton kasa suke yi alheri ne – Alhaji Muhammed Khalid Kwantagora
Alhaji Muhammed Khalid Kwantagora, “Idan ‘yan siyasa suna ficewa daga jam’iyunsu suna komawa wasu jam’iyu domin hangen lalacewar al’amura da za su iya jefa kasa cikin halin kaka ni ka yi, kuma idan suna yin haka ne tsakaninsu da Allah domin tserar da kasa daga mawuyacin hali, to ai babu laifi yin haka yana da kyau, amma ba kamar irin yadda tsofaffin Gwamnonin Sakkwato da Kano suka yi ba wanda irin nasu canja shekar ta yi daban, domin kowa ya sani cewa, sun yi hakan ne domin cimma burin kansu, amma ba domin kishin kasar haihuwarsu da ci gaban al’ummarta ba.”