Canjin sheka a tsakanin ’yan siyasar kasar nan alheri ne ga dimokuradiyya? 4

Yadda canjin sheka ya zama ruwan dare a tsakanin ‘yan siyasar kasar nan ta sa wakilanmu suka bazama don jin ra’ayoyin jama’a a kan haka. Ga ra’ayoyin kowane daga  ciki kamar haka Canjin sheka alheri ne – Auwalu Sidi Sunana Auwalu Sidi. Shi dai wannan canje-canjen sheka daga wata jam’iyya zuwa wata daban da kaga […]

Canjin sheka a tsakanin ’yan siyasar kasar nan alheri ne ga dimokuradiyya? 4
Canjin sheka a tsakanin ’yan siyasar kasar nan alheri ne ga dimokuradiyya? 4

Yadda canjin sheka ya zama ruwan dare a tsakanin ‘yan siyasar kasar nan ta sa wakilanmu suka bazama don jin ra’ayoyin jama’a a kan haka. Ga ra’ayoyin kowane daga  ciki kamar haka

Canjin sheka alheri ne – Auwalu Sidi

Sunana Auwalu Sidi. Shi dai wannan canje-canjen sheka daga wata jam’iyya zuwa wata daban da kaga wasu ‘yan siyasa ke yi a kasar nan yau, suna yi ne saboda sun gano cewa jam’iyyar da suke da bata nuna adalci ga al’ummar da suka zabe su.  Shi ya sa suke canja sheka. Saboda haka a nawa ra’ayi dai haka ka iya zama alheri ga kasar nan da su kansu ‘yan siyasar,  wato mutane irin su Janar Muhammadu Buhari. Haka ka iya kare mutuncinsu a idon talakawa. Saboda haka a gani na alheri ne. kuma adu’ar da muke musu shi ne Allah yasa da gaske suke yi. Kada a canja sheka daga baya maimakon a ga canji sai a ci gaba da halin da.