Capri-Sun ya kirkiro sabon samfuri

Kamfanin Capri-Sun da ke yi kayan sha da tande-tande ya kirkiro sabon samfuri mai girman mililita 100 domin samar da samfuri mai girma da biya wa abokan huldarsu bukata. Wannan sabon samfurin za a rika sayar da shi a sari a farashin Naira 50, wanda kamfanin ya ce ya yi hakan ne domin abokan hukdarsa […]

Capri-Sun ya kirkiro sabon samfuri
Capri-Sun ya kirkiro sabon samfuri

Kamfanin Capri-Sun da ke yi kayan sha da tande-tande ya kirkiro sabon samfuri mai girman mililita 100 domin samar da samfuri mai girma da biya wa abokan huldarsu bukata.

Wannan sabon samfurin za a rika sayar da shi a sari a farashin Naira 50, wanda kamfanin ya ce ya yi hakan ne domin abokan hukdarsa su samu zabin abin da suke bukata.

Kamfanin ya ce sabon samfuri yana dauke da dandano irin na sauran samfurin, kuma  yana saukin dauka da saukin rikewa ko sanyawa a aljihu. Sannan yana dauke da sinadarai masu inganci da kara lafiya da sanya jin dadi da natsuwa.

A yanzu haka sabon samfurin yana zuwa ne a samfurin lemu da tuffa kawai.

A cewar Manajan Daraktan Kamfanin Chi Limited, Deepanjan Roy, samfurin Capri-Sun mai girman mililita 100 an tsara yadda ya fita daban domin jin dadin abokan hulda.

“Wannan sabon samfuri zai samar da jin dadi da dandano na daban. Kuma zai zama abin sha wanda yara za su fi kauna a Najeriya. Yanayin samfurin mai girman mililita 100 zai ba abokan hulda sha’awa matuka musamman wadanda suke son samfurin da za su iya dauka su rike a hannu cikin sauki,” inji shi.

Za a iya samun samfurin Capri-Sun din guda 40 a cikin katan kamar sauran samfurin, kuma za a iya samu a duk kantunan sayar da Capri-Sun a duk fadin Najeriya.

Capri-Sun abin sha ne da iyaye mata suke son shayar da ’ya’yansu a Najeriya saboda dandanonsa mai dadi, kuma ana hada shi ne sinadarai na ainihi masu inganci ba tare da hadawa sinadaran kanti ba.