Carbalho ya zama sabon Shugaban Sao Tome
Masu kada kuri’a kasar Sao Tome da Principe sun zabi tsohon Firaministan kasar Ebaristo Carbalho a matsatin sabon shugaban kasar, wanda take yankin yammacin Afirka.Sai dai a wani mataki na ba safai ba, shugaban kasar Sao Tome and Principe Manuel Pinto da Costa wanda shi ma yake takara ya kauracewa zaben shugaban kasar na zagaye […]
Masu kada kuri’a kasar Sao Tome da Principe sun zabi tsohon Firaministan kasar Ebaristo Carbalho a matsatin sabon shugaban kasar, wanda take yankin yammacin Afirka.
Sai dai a wani mataki na ba safai ba, shugaban kasar Sao Tome and Principe Manuel Pinto da Costa wanda shi ma yake takara ya kauracewa zaben shugaban kasar na zagaye na biyu, lamarin da ya bai wa babban abokin hamayyarsa nasara.
Mista Costa ya janye daga shiga zaben ne, wanda aka gudanar ranar Lahadi, yana zargin cewa an tafka magudi a zagayen farko na zaben da aka yi ranar 17 ga watan Yuli.
Daga nan ne, babban abokin hamayyarsa, wato Mista Carbalho ya samu tabbacin lashe zaben.
Ya samu kashi 49.8 cikin 100, yayin da Mr Pinto da Costa ya samu kashi 24.8 cikin 100 na kuri’un da aka kada.
Ana zargin Mista Costa da gallazawa ‘yan kasar a shekara 15 da ya kwashe yana mulkin kasar, wacce ta samu ‘yancin kanta daga Portugal a shekarar 1975.