Casawa da lallasawa

kungiyoyin dukan ta-mola da harbatta-mati na kasashen Turai sun juyar da alkiblar karatun wasikar jakin dawa da na gida da matasan Haurobiya ke yi, ind amafi yawancinsu ke tarewa a gaban akwatin magan mai hoto, don baje na-mujiyarsu su g ayadda ake yin zari ruga tsakanin Casawa-da-lallasawa da Munin-bayan ta-mola ko su jinbirin-tus da madarar […]

Casawa da lallasawa
Casawa da lallasawa

kungiyoyin dukan ta-mola da harbatta-mati na kasashen Turai sun juyar da alkiblar karatun wasikar jakin dawa da na gida da matasan Haurobiya ke yi, ind amafi yawancinsu ke tarewa a gaban akwatin magan mai hoto, don baje na-mujiyarsu su g ayadda ake yin zari ruga tsakanin Casawa-da-lallasawa da Munin-bayan ta-mola ko su jinbirin-tus da madarar kwallo da sauransu. Wannan ta’adda da matasa masu jini a jika suka dauka, ta haifar da ce-ce-ku ce a wuraren kwadago don neman kadago.

Al’amarin ta-mola ya kasura, ya tumbatsa a doron dunya. Wannan kuwa duk bai ras anasaba da damnin dalar Hauron Amurkawa ko fama-faman Birtaniya da gwanayen dukan ta-mola ke cika lalitarsu da dimbin makudan matssabbai. Hakika idan na dubi yadda ake yin cincirindo wajen kallon tamola a akwatunan Magana, musamman idan na ji an kaure da takaddama kan matasan da Murhun-hoho ke horarwa, sai in rike baki, domin ni a ganina hakan bai dace. Kuma na sha bijiro wa kaina da ayar tambaya kan ko matasanmu bas u san akwai dimbin kalubale a gabansu ba, musmaman a wannan zamani da guguwar sauyin salon wasan-Samson-siya-siya, a tsakanin mai dan boto da sanda jirge da kuma jam’in jama’ar jam’iyya mai maganin zogi da radadin kurungu?
Haurobiyawa ku ja na-zomon matasa masu jini a jika su yi saisa-saisa wajen bibiyar tamola ko dukan harbatta-mati. Ku sani masu dukan tamola a kasashen da ake murguda baki kamar an ci kilishi, snanan a kan ga gilashi, a yi ta yaren Ingilishi, ai rayuwarsu na da laushi, sabanin harkokin mutanen Ifrikiyya da ke gani dushi-dushi. Abin d akawai nike son nusar da matasanmu a nan shi ne mafi yawan masu harbatta-mati suna da wata sana’a ko kwarewa a fannonin rayuwa, inma bas u da ita hukumomin kasashensu subn tsara yadda za a kashe musu karsashin kuncin rayuwa, amma mu kuwa masu kwashi-kwaraf sun yi wa lalitar kasar mu karkaf. Don haka ma Baban masu Burin-huriyya keta fafutikar kwato dimbin dukiyar da aka yi sabi-zarce da ita.
Kuma har yanzu da zarar mutum ya kamala koyon watsattsaken bobo da kwambon bokoko, sai kawai ya zuba wa gwamnatin Haurobiya na-mujiya wai yana jiran ta lalubo masa hanyoyin neman kadago a wajen kwadago. Kai hasalima wadanda suka kammala karakaina a jam’in jam’ar jami’o’i sai kaji babu abin da suke nema sai kwadon farar kwala, al’amarin da kan kaisu ga cin kwalar samarin kusu da ’yan matan jaba da gafiya.
’Yan makarantar da suka fasko batuna akan tamola, to ina son su nusar da yaran Gizo-gizon-dakin-gwaggo cewa, kamata ya yi su kama sana’ar na-duke ko su yi limbu-limbu a cikin lambu, ta yadda za su bayar da gudunmuwarsu a wajen samar wa al’ummar kasar nan kayan dundume kururu, tun kafin ’yar babban birnin Jihar Zaman-fara ta fyade su. Malam mai yaren Hau-hau wajen hawan sa ba tare sa-in-sa ba, ya sha furta cewa, “da ruwan tumbi ake jan na kwakware.”
Ba tare da na cika ku da surutu rututu ba, kamar Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters, ina ganin yadda kasashen Turai suka samu kungiyoyin tamola irin su Cassawa-da-lallasawa, to akwai yiwuwar matansmu su karke da kungiyar Kasawa-da-kassarawa; ko madarar-kwallon su ta zame mana madarar kwalla; Jinbirin-tus din su ta zame mana jibar-tusa.
Haurobiyawa, wani abin farin ciki da nike son ku sani shi ne, akwai ’yan dugwi-dugwi abokan man-kaza da suka dauki gargadin da muka sha yi a wannan farfajiyar makaranta, don haka sun ci gaba a rayuwarsu. Kusan kow aya san cewa, tsohon mai adawar takaddama da wannan makaranta, wato mai motar roba, yana can yana laluben na-koko a cikin wayoyin lantarki. To, da ya tsaya a harkar tamola, ya za a yi ya taka wannan matsayi. Ga shi Malam Nakwaciri sai rokon Mai-duka yake yi mana don mu samu nasara a harkar watsattsake da buda wagagen littattafai. Ga Shehin Sunduki can ya koma Jihar Bararon-nono, babban birnin su Aln-guburo. Wadannan mutane da na jero muku da cewa, su ba “dodanni ba ne,” ai makaranta ta yi trasiri a rayuwarsu.
Lallai mu yi karatun ta-natsu, ta yadda za mu mamaye duniya kamar yadda mutanen Hutsanyu suka yi wa kowace harka kawanya. Su Hutsanyu masu tsalle bisa tsinin mashi, kowa ya san mutanen Mawo Tsedong ne. ba sai na yi karin haske ba, tunda sun kusa mamaye Haurobiya, amma ku matasa kuna nan kuna zaman kasha fatari da harbatta-mati.
Yau al’amuran da ke faruwa a kasar Haurobiya ba a damawa da ku, domin mafi yawancinku hankalinku a hannun taguwa yake, shi yasa muka yanke cewa, ‘da tsohuwar zuma ake magani.’ Kuna dai ganin irin aikin da Tsoho maid aka wa yaro kashe ke aiwatarwa a Haurobiya. Wadanda suka samu kwadagon farar kwala a wajen laluben kadago, to su kiyayi kwashi-kwaraf, musamman ma ganin hukumar Gogargama sha gwagwarmaya da arangama d amasu fashi da mukami ko da dabara ta fara kazarkazar.
Uwa-uba zan karkare da tunasar da GizBaba cewa, a lokacin da ya yunkura ya tunatar da jiga-jiga shugabannin Kamfanin Buga Amintattun jaridun kasar Haurobiya kan lallai su yi wa ’yan kwadago girkin ca’ammas, musamman idan aka ce an zaftare wa’adin huta-fara da kwanaki sili da karamin lauje, sai babban jami’in aiwatar da ayyuka a wannan kamfani ya yi masa korafi kan yadda ’yan kwadago ke baje na-mujiyarsu a gaban akwatunan maga masu hoto don kallon harbatta-mati. Kai wannanb babban jami’I har ya bijiro da anaiyarsa ta cire akwatunan magana da ke nuna hotunan tamola. Kuma idan ban kakaba wa kurunguna tagiyar malam Mantau ba, na san a tsakanin shekara ta dubu karamin lauje da sili da karamin lauje zuwa ta dubu karamin lauje da sili da kofar hanci, Maimartaba Bahagon Babban mutum mai rawani na birnin Mina-mina da ke Jihar Ni-na-ja, ya zargi tamola da kade-kade da raye-raye a kan yawan cin kasar da aka yi a jarrabawar watsattsaken nakoko.