CBN da Bill Gates sun hada hannu don tsoma ’yan Najeriya a harkar kudi

Mista Folashodun Shonubi ya nanata shirin bankin na hada hannu da Gidauniyar BMGF da sauran abokan ci-gaba.

CBN da Bill Gates sun hada hannu don tsoma ’yan Najeriya a harkar kudi

Babban Bankin Najeriya CBN da Gidauniyar Bill and Melinda Gates (BMGF) sun yanke shawarar hada hannu don karfafa shigar da mutane cikin harkokin banki a Najeriya.

A cewar wata sanarwa da Babban Bankin ya fitar a makon da ya gabata, ganawar da aka yi a Abuja ta tabo yunkurin cibiyoyin biyu na samar da sababbin hanyoyin karfafa samun kudade ga jama’a.

A lokacin ganawar Mukaddashin Gwamnan CBN, Mista Folashodun Shonubi, ya nanata shirin bankin na hada hannu da Gidauniyar BMGF da sauran abokan ci-gaba.

Ya nuna jin dadi kan ci gaban da aka samu a sassa da dama na sanya jama’a a harkokin kudi, inda Mista Shonubi ya nanata cewa har yanzu akwai matsalolin da suke hana cim ma nasarar da ake bukata a tsoma jama’a a harkokin kudin, inda ya yi kiran a samu babban hadin kai a tsakanin CBN da Gidauniyar BMGF don magance wadannan matsalolin yadda ya kamata.

Mista Shonubi, wanda ya samu rakiyar Misis A’ishah Ahmad, Mataimakiyar Gwamnan mai kula da Daidaiton Tsarin Kudi (FSS), ya bayyana muhimmancin hadin gwiwa a tsakanin CBN da Gidauniyar BMGF wajen jagorantar tsoma dukkan nau’o’in jama’ar Najeriya a harkokin kudi ta banki.

Da yake jawabi a taron, Mista Bill Gates, Shugaban Hada-ka na Gidauniyar Bill and Melinda Gates Foundation, ya bayyana sassan da gidauniyar za ta mayar da hankali wajen ci gaba da hada hannu da Najeriya a fannonin da suka shafi kiwon lafi ya da aikin gonad a harkokin kudi.

Mista Gates ya nuna gamsuwa da nasarar da gidauniyarsa ke samu wajen gudanar da ayyukan ci-gaba a Najeriya.

Yayin da ya tabo wasu matsaloli da gibin da ke akwai, ya ce yana da yakinin samun kyakkyawar makoma ga kasar nan inda ya kawo misali da sababbin tsare-tsaren kudi da tattalin arziki da ake yi yanzu.

Babu sojojin ƙasar waje a yankinmu —Sakkwatawa

Yadda dagacinmu ya sassara ni da adda — Maraya

Bidiyoyin da suka ɗauki hankalin ’yan Najeriya a 2024

An kama mutum 859 da ceto 46 da aka yi garkuwa da su a Filato – ’Yan sanda