CBN ya fito da kai’idojin amfani da e-Naira
Ka’idojin za su shafi cibiyoyin hada-hadar kudade da daidaikun mutane.
Babba Bankin Najeriya (CBN) ya fitar da wasu kai’idoji da sharuda da ya kamata a sani domin yin amfani da tsarin kudin intanet na e-Naira.
Aminiya ta gano cewa ka’idojin amfani da e-Naira za su shafi duk cibiyoyin hada-hadar kudade da kuma daidaikun mutane kamar yadda ya zo a cikin bayanin da CBN ya fitar.
- Mai kamfanin Facebook ya tafka asarar Dala biliyan 7
- Kudin e-Naira: Ma’ana, fa’idoji da tsarin gudanuwarsa (1)
Ka’idojin sun hada da: kafin fara amfani da tsarin, dole za a bayyana yadda za a yi amfani da walet din e-Naira, ko amfanin mutum daya ko a matsayin amintattu.
A karkashin Dokar CBN ta 2007 da Dokar Bankuna da Sauran Cibiyoyin Kudi (BOFIA) ta 2020 ne kadai ke da alhakin lura da kuma raba kudin.
Darajar e-Naira za ta kasance daidai da ta Naira, za su rika tafiya kafada da kafada, kuma a karkashin kulawar CBN.
A cikin e-Naira walet ne kadai za a iya amfani da shi wannan kudin, sannan za a iya canza shi zuwa sauran kudaden duniya.