CBN ya musanta yunƙurin ƙirƙirar sabbin takardun Naira a baɗi

CBN ya ce sakon ba haka yake ba saboda haka an fahimce shi ne a baibai.

CBN ya musanta yunƙurin ƙirƙirar sabbin takardun Naira a baɗi

Bandur-bandur na sabbin takardun kudin Naira

Babban Bankin Najeriya CBN ya ce ba shi da wani shiri na sake ƙirƙiro wasu sabbin takardun naira a shekara mai zuwa.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da daraktan sadarwa na CBN, Isa Abdulmumin ya fitar ranar Talata.

Sanarwar ta bukaci ’yan Najeriya su yi watsi da wani takaitaccen sakon waya da ake yadawa, wanda ke nuna cewa CBN na shirin sake bullo da sabbin takardun naira a shekara ta 2024.

Abdulmumin ya nunar cewa sakon ba haka yake ba saboda haka an fahimce shi ne a baibai.

“Mun shiga damuwa game da wannan batu, wanda muka musanta tun ba yanzu ba, amma ga alama yana samun karbuwa da muhawara masu yawa a kan illar irin wannan manufa ga tattalin arzikin Najeriya.

CBN ya ce “Muna son jaddada cewa bayanin da ke cikin wannan sako, ba haka yake ba.”

Ya kara da cewa masu wallafa sako a yunkurinsu na jamhuru, sun jirkita rubutun daga wata tsohuwar manufa ta gwamnan CBN na baya a shekara ta 2007, amma sai suke bayyana shi tamkar yanzu ya faru.

Ya dai nanata cewa a yanzu babu wani shiri na sake fasalin takardun kudin kasar.

Tinubu ya yi naɗin sabbin muƙamai huɗu

Majalisar Zartarwa ta amince da kusan Naira tiriliyan 50 Kasafin Kuɗin 2025

Tinubu ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa

HOTUNA: Ana shirye-shiryen jana’izar marigayi Lagbaja