CBN ya nada sabbin shugabannin bankunan Union, Keystone da Polaris

sabbin nade-naden sun fara aiki ne nan take

CBN ya nada sabbin shugabannin bankunan Union, Keystone da Polaris

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya nada sabbin shugabannin bankunan Union da Keystone da Polaris.

CBN ya nada sabbin shugabanni da manyan daraktocin bakunan ne sa’o’i kadan bayan ya sanar da rushe majalisar daraktoci da kwimitin gudanarwan bankunan.

Da take sanar da hakan a safiyar Alhamis, Daraktar yada labaran CBN, Hakama Sidi Ali, ta ce sabbin nade-naden sun fara aiki ne nan take.

Hakama Sidi Ali ta ce CBN ya nada Yetunde Oni a matsayin sabuwar Manajan Darakta kuma Shugabar Bankin Union, Mannir Ubali Ringim kuma Babban Daraktan Gudunarwa na bankin.

Bankin Keystone kuma, Hassan Imam shi ne sabon Manajan Darakta kuma Shugaba, tare da Chioma Mang a matsayin Babban Daraktan Gudunarwa.

A Bakin Polaris kuma, Lawal Mudathir Omokayode Akintola ne sabon shugaba kuma Manajan Darakta, Daraktan Gudunarwansa kuma Chris Ofikulu.

Babban Bankin ya sanar da sabbin nade-naden a ranar Alhamis ne washegarin da ya rushe kwamitocin daraktocin bankunan kasuwancin.