CBN ya soke harajin tura kudi ta intanet

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya dakatar da karbar harajin tura kudi ta intanet.

CBN ya soke harajin tura kudi ta intanet

Injin POS

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya soke sabon harajin tura kudi ta intanet da ta bullo da shi a kwanakin baya.

A kwanakin baya ne CBN ya ɓullo da sabon harajin mai suna Harajin Tsaron Intanet, na kashi 0.5% kan duk kudin da aka tura ta intanet.

“Muna sanar da bankunan kasuwanci da sauran cibiyoyin haɗar kudaden cewa, mun janye umarnin da muka bayar na farko kan cirar harajin 0.5% na tsaron intanet daga masu tura kudi ta intanet,” in ji CBN.

Janye sabon harajin da ya ja wa babban bankin kakkausar suka daga al’ummar Najeriya na kunshe ne a cikin wata sanarwa da bankin ya fitar mai dauke da sa hannun Chibuzo Efobi, Daraktan Sashe Kula da Tura Kudade da kuma Mustafa Haruna, Daraktan Sashen Kula da Tsare-tsaren kudade.

Sanarwar na dauke da kwanan watan 6 ga watan nan na Mayu, 2024.

Ana iya tunawa wasu shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci CBN ya soke harajin, wanda majalisar dokoki ta kasa ta kira da rashin tausaya wa ’yan Najeriya.

Majalisar ta bayyana cewa babban bankin bai fahimci sashen dokar da ya yi amfani da shi wajen ɓullo da sabon harajin ba,

Don haka ne ma majalisar wakilai ta umarci kwamitinta da ya yi wa babban bankin karin haske kan tanadin dokar tsaron intanet.

A baya dai CBN ya bayyana cewa dokar tsaron intanet ce ta tanadi hakan inda za a rika tura kudin zuwa ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro domin gudanarwa.

 

Zazzaɓin Lassa: Mutum 190 sun mutu, 1,154 sun kamu a 2024 – NCDC

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai