CBN ya rushe Bankin Heritage
Babban Bankin Najeriya ya soke lasisin Bankin Heritage nan take.
Babban Bankin Najeriya (CBN) ya soke lasisin Bankin Heritage nan take.
CBN ya sanar da soke lasisin bankin kasuwanci na Heritage ne a sakamakon rashin katabus.
Sanarwar da kakakin CBN, Halima Sisi Ali, ta fitar ta ce rushe bankin Heritage ya zama dole saboda “Majalisar Daraktoci da hukumar gudanarwar bankin sun kasa farfado da shi.
“Lmarin ya wayi gari a matsayin barazana a harkar hadahadar kudade,” wanda hakan ya saba sashe na 12 (1) na dokar gudanar da bankuna (BOFIA, 2020).
- NLC ta kashe wuta daga babbar cibiyar lantarkin Najeriya
- Yajin aiki: Maniyyatan Najeriya na cikin rashin tabbas
“Duk kokarin CBN da kuma dama da matakan da aka dauka na shawo kan lamarin, ya gagara, don haka babu wani zabi face CBN ya kwace lasisin,” in ji sanarwar.
Ta ce yin hakan ya zama dole domin ba wa masu hulda da bankuna kwarin gwiwa game da bangaren a Najeriya.
Ta kara da cewa an ba wa Hukumar Inshorar Kudade (NDIC) alhakin cefanar da bankin na Heritage domin takaita asarar kwastomomi da masu zuba jari a bankin.