CBN ya soke lasisin ’yan canji 4,173 a faɗin Nijeriya

Daga cikin waɗanda abin ya shafa akwai masu bijire wa umarnin Babban Bankin kan tsare-tsarensa.

CBN ya soke lasisin ’yan canji 4,173 a faɗin Nijeriya

Ginin Hedikwatar Babban Bankin Najeriya

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar da soke lasisin gudanar da ayyuka na wasu ’yan canji 4,173 a faɗin ƙasar nan take.

CBN ya ce daga cikin ’yan canjin da soke lasisin ya shafa akwai waɗanda suka gaza sabunta lasisinsu, da waɗanda suka gaza biyan wasu caje-caje kuɗin gudanarwa da Babban Bankin ya rataya a wuyansu.

Haka kuma, daga cikin waɗanda abin ya shafa akwai masu bijire wa dokokin Babban Bankin kan tsare-tsarensa na yaƙi da safarar kuɗaɗen haram, dakile fitar da kuɗaɗen da ke ɗaukar nauyin ayyukan ta’addanci, da kuma dakile ka’idojin samar da kuɗaɗe.

Kazalika, CBN ya ce waɗanda aka soke wa lasisin akwai masu rashin mika wa CBN ɗin bayanan yadda suke sayar da dalar duk mako.

Wannan matakin wani ɓangare ne na ƙoƙarin da CBN da Gwamnatin Tarayya ke yi na maido da ƙwarin gwiwa a kasuwar canji da musayar kuɗaɗen waje da kuma farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar.

CBN dai ya yi alƙawarin ci gaba da bayar da dala ga masu kamfanin canjin kuɗin a kowanne mako kamar yadda aka saba a baya.

Sai dai ya kuma lashi takobin hukunta duk wanda ya saɓa ƙa’idar da aka shimfida ta gudanar da hada-hadar a Najeriya.

Gwamnatin Kano na shirin tara harajin 80bn a 2025

Kirsimeti: Zulum ya ɗauki nauyin jigilar fasinjoji 710 zuwa garuruwansu

Ɗan shekara 60 ya rasu a hatsarin kwalekwale a Sakkwato

Yadda gobara ta ƙone kasuwar babura a Zamfara