CBN zai ba wa manoma bashi mara ruwa

Babban Bankin Kasa (CBN) ya bullo da sabbin tsare-tsaren harkokin kudi da za su ba manoma da masu matsakaita da kananan sana’o’i damar karbar bashi mara ruwa. Bankin dai ya fitar da sabbin sharuddan basukan marasa ruwa ne ranar Talata 14 ga watan Yuli. Kwararru da masana harkar kudi sun ce sabon tsarin zai bayar […]

CBN zai ba wa manoma bashi mara ruwa

Wasu manoma a gona

Babban Bankin Kasa (CBN) ya bullo da sabbin tsare-tsaren harkokin kudi da za su ba manoma da masu matsakaita da kananan sana’o’i damar karbar bashi mara ruwa.

Bankin dai ya fitar da sabbin sharuddan basukan marasa ruwa ne ranar Talata 14 ga watan Yuli.

Kwararru da masana harkar kudi sun ce sabon tsarin zai bayar da damar amfana ga wadanda ba sa son bashi mai ruwa ko kuma bas u da kadarorin da za su gabatar a matsayin jingina.

Matakin dai ya zo ne biyo bayan shawarar da babban bankin ya yanke a watan Yunin bana bayan wata tattaunawa na shigo da bangarorin tattalin arzikin da ba sa mu’amala da rance mai ruwa da nufin tallafawa kananan sana’o’i musamman wadanda annobar COVID-19 ta fi yi wa illa.

Sharudan da CBN ta shimfida sun wajabta wa bankuan marasa ta’ammali da kudin ruwa sadaukar da kaso biyar cikin 100 na ribarsu ta shekara bayan cire haraji ga asusun da aka ware domin shirin.

Wadanda suka cancanta su ci gajiyar shirin sun hada da kananan kamfanonin masu alaka da harkar noma, samar da kayan aikinsa, adanawa ko kuma kasuwancinsa, inji CBN.

“Babban makasudin shirin rance mara ruwa shi ne shigar da akalla matasa 370,000 nan da 2023 cikin harkar noma a fadin kasa da nufin rage zaman kasha wando.

“Shirin na da burin ganin karin matasa yan shekaru 18 zuwa 35 sun rungumi harkar noma gadan-gadan ta hanyar hadin gwiwa da gwamnatocin jihohi, CBN da sauran masu ruwa da tsaki don habaka harkar samar da abinci a kowacce jiha”, inji CBN.

‘Tallafin zai taimaka wa masu karamin karfi’

Da yake tsokaci a kan shirin, babban limamin Masallacin Juma’a na Al-Furqan da ke Kano, Dakta Bashir Aliyu Umar wanda ya yi mu’amala da shirin ya ce, “CBN ya dade yana bayar da rancen kudade ga banagarorin tattalin arziki irinsu harkokin noma, harkokin da ba na man fetur ba, harkar masaku da kuma matsakaita da kananan sana’o’i.

“Kawai babbar matsalar ita ce yawanci irin wadannan basussukan sukan zo da ruwa.

“Ko da yake dai yawanci za ka ga ruwan ba shi da yawa, amma dai komai kankantar shi za ka ga yakan zo wa Musulmi da tarnaki da yawanci ba za su iya cin gajiyar shi ba.

“Dalilin da ya sa kenan za ka ga talauci ya fi kamari a Arewacin Najeriya saboda sana’o’i ba sa samun tallafi ko bashi.

“Ko da ka yi niyyar ba su bashin, ko da wace manufa ka bullo matukar akwai ruwa a ciki komai kankantarsa za ka ga ba za su karba ba”, inji Dakta Bashir.

Ya kara da cewa yawancin basussukan ba su bukatar gabatar da wata kadara kafin a samu.

“Kawai abun da ake bukata shi ne wata takardar shaida, kamar takardar kammala yi wa kasa hidima ta NYSC, amma fa dole sai mutum na da rubutaccen tsarin yadda zai gudanar da kasuwancin nasa.

“Wannan ba karamin ci gaba ba ne, CBN ya amsa koke-koken al’umma”, inji shi.