CBN zai daina bai wa bankuna Dala
Tuni CBN ya sanar da bankuna cewa su yi ta kansu wajen samun Dala da sauran kudaden kasar waje
‘Yan canji na kokawa da matakin CBN
Hoto:
REUTERS
Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar da shirinsa na daina bayar da kudaden kasashen waje ga bankunan kasuwanci.
Da yake sanar da hakan, Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya ce lokaci ya yi da bankunan kasuwanci za su yi ta kansu wajen samun kudaden kasashen waje ta hanyoyi da daban-daban.
- ’Yan fashi sun kashe ’yan sanda, sun wawushe kudi a motar kudi
- Dalilan da ya sa ba a cika samun Hausawa ba a Super Eagles
“Zuwa karshen shekarar nan za mu ce wa bankuna kar su kara zuwa wurin CBN neman kudaden waje, su je su nemo mutanen da ke son fitar da kaya daga kasar nan, idan suka zo za ku iya ce musu kuna son Dala miliyan 200.
Emefiele ya shaida wa taron bude shirin RT200 cewa tuni dai bankin ya sanar da bankunan shirin sa dakatar da ba su kudaden kasashen wajen daga karshen shekarar 2022 da muke ciki.
Ya sanar da matakin ne a ranar Alhamis, watanni kadan bayan bankin ya soke bayar da kudaden kasashen waje ga ’yan canji, suka koma bayarwa ga bankunan kasuwa.
Wasu masana harkar tattalin arziki sun bayyana cewa idan har aka aiwatar da sabon tsarin da CBN ta bullo da shi, hakan zai taimaka wajen kare darajar Naira daga karyewa.
Zai kuma taimaka wajen samar da ayyukan yi, bunkasa masana’antu, fitar da kayan da ake samarwa a Najeriya zuwa kasashen waje da kuma samar da kudaden kasashen waje a Najeriya.
Masana sun bayyana cewa, tun a lokacin da CBN ya dauki matakin hana ’yan canji kudaden kasashen waje, ya ja hankalin bankin cewa, wannan din kadai ba zai magance matsalar ba, sai idan bankin ya dauki matakan da suka shafi kowan bangaren da abin ya shafa, ciki kuwa har da bin diddigin abin da bankuna ke yi da kudaden da ake ba su.