CBN zai koma ba wa ’yan canji Dala a kan N1,301

CBN zai rika ba wa ’yan canji Dala a kan N1,301, amma ya kayyade ribar da za su dora a kai

CBN zai koma ba wa ’yan canji Dala a kan N1,301

Babban Bankin Najeriya ya kayyade wa ’yan canji yadda za su rika sayar da Dala, da kuma ribar da za su dora.

A ranar Talata babban bankin ya sanar da hakan tare da cewa zai rika ba wa kowane dan canji mai rajista kudaden kasashen waje da kimarsu ta kai Dala N20,000 a kan kowace Dala, N1,301.

“Ribar da za su dora ba zai haura kashi daya cikin 100 na farashin da suka samu kudaden kasashen wajen daga hannun CBN ba,” in ji sanarwar mai dauke da sa hannun Daraktan Kasuwanci da Musayar Kudade na CBN, Hassan Mahmud.

Hakan na zuwa ne kimanin shekaru biyu da CBN, a karkashin jagorancin tsohon shugabansa, Godwin Emefiele, ya dakatar da ba wa ’yan caji kudaden kasar wajen.

Amma sabuwar sanarwar ta ce bankin ya lura tsohon tsarin ya haifar da tazara mai yawa a farashin Dala a hukumane da kuma a wurin ’yan canji.

A cewar sanarar, ana sa ran sabon matakin ba wa ’yan canji Dala zai hana tashin gwauron zabon da take yi da kuma rage bambancin tsakafin farashin gwamnati da na ’yan canji.