Cece-ku-ce ya hana ni zama kocin Italiya — Andrea Pirlo

Rahotanni sun ce tsohon kocin Italiya Antonio Conte yana ɗaya daga cikin manyan waɗanda ake tunanin za su karɓi aikin.

Cece-ku-ce ya hana ni zama kocin Italiya — Andrea Pirlo

Tsohon fitaccen ɗan wasan Italiya, Andrea Pirlo, ya bayyana takaicinsa kan yadda cece-ku-cen da aka riƙa yi kan sunansa ya hana shi zama sabon kocin tawagar ƙwallon ƙafar ƙasar.

Pirlo mai shekara 47 ya ce ya samu labarin cewa an cire sunansa daga cikin jerin masu neman kujerar ne a ranar Lahadi.

Sai dai ya ce abin da ya fi ba shi haushi shi ne yadda aka riƙa tattaunawa kan alaƙarsa da wani kamfanin caca na Rasha, maimakon a yi masa hukunci bisa tarihin aikinsa na horarwa.

Pirlo ya taka muhimmiyar rawa wajen taimaka wa Italiya lashe Kofin Duniya a 2006, amma bai samu manyan nasarori ba tun bayan fara aikin horarwa, inda ya lashe Kofin Italiya guda ɗaya kacal da Juventus.

Shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafar Italiya (FIGC), Giovanni Malagò, ya ce za a sanar da sabon kocin tawagar ƙasar nan ba da jimawa ba.

Rahotanni sun ce tsohon kocin Italiya Antonio Conte yana ɗaya daga cikin manyan waɗanda ake tunanin za su karɓi aikin.