Ceto Tafkin Chadi
Akwai rahotanni a baya-bayan nan da bincinken kwararru kan Tafkin Chadi da ke da daga hankali, sakamakon barazanar da mutum miliyan 30 da suke dogaro da shi suke fuskanta ta rasa hanyar samun abincin da suke rayuwa da shi. Ruwan tafkin na da muhimmanci ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin kasashen da ke […]
Akwai rahotanni a baya-bayan nan da bincinken kwararru kan Tafkin Chadi da ke da daga hankali, sakamakon barazanar da mutum miliyan 30 da suke dogaro da shi suke fuskanta ta rasa hanyar samun abincin da suke rayuwa da shi. Ruwan tafkin na da muhimmanci ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin kasashen da ke yankin wanda haka ne ya sa aka kafa Hukumar Kula da Tafkin Chadi (LCBC) shekaru da dama da suka gabata don ta rika lura da shi tare da albarakatunsa.
Don haka babu shakka abishir ne mai dadi da zababben Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi alkawarin sadaukar da dukiya tare da hada hannu da kasashen makwabta domin ceto koma bayan da tafkin yake yi.
A cewar binciken masanan ruwan Tafkin Chadi na ja baya a bangaren zurfi da fadi ma’ana yana cikewa a cikin shekara 50 da suka gabata ba tare da ana dauka wasu matakai na dakatar da hakan ba.
Baya ga ’yan Najeriya, fiye da mutum miliyan 40 ’yan Afirka da ruwan tafkin ya ratsa yankunansu ko suke zaune a gabarsa kai-tsaye suke dogaro da ruwa da albarkatunsa wajen gudanar da rayuwarsu.
Daga 1964 lokacin da Najeriya da Kamaru da Chadi da Nijar suka kafa Hukumar LCBC don kula da ruwan tafkin da hanyoyin da yake bi, bayanai sun nuna ruwan ya yi kasa da kusan kashi 90 cikin 100 a doron kasa daga yanki mai girman kilomita dubu 25 ya dawo kimanin kilomita dubu 2 sakamakon shekarun da aka dauka ana fama da fari da kwararowar hamada da kamfan ruwa ke haifarwa sai iska da tsananin zafi da yankin Sahel ke fama da shi. Kusan duk hanyoyin ruwa da ke yankin ko dai sun kafe kwata-kwata ko suna daf kafewa.
Kuma yayin da tafkin ke kafewa, mutanen da suke cin gajiyarsa sun rika hijirar tilas daga yankin suna komawa hatta wuraren da ba su da inganci yanayi inda suka rika yin fama da rikice-rikice a kan iyakokin kasashen yayin yin haka. Manoma da masunta suna fuskantar wannan matsala ta kafewar ruwan, inda mazauna yankin dubu 58 wadanda galibinsu mutanen Chadi ne da Najeriya da suke zaune a tsibirin da ke cikin tafkin.
Matsalar tana iya zama mai saukin fuskanta da gwamnatocin yankin sun dauki kwararan matakai a baya don magance ta. Ya wajaba kasashen da suke yankin tafkin su ayyana dokar ta-baci domin maganace wannan babbar matsala. Akwai bukatar a mike tsaye sosai a sake farfado da tafkin.
In kuma bah aka ba, bakin talaucin da ake fama da shi a yankin zai dada karuwa, ta yadda za a samu karuwar rashin zaman lafiya da tayar da kayar baya a tsakanin jama’a, a dada samun koma bayan tattalin arziki da karuwar yawan jama’ar da ake rabawa da muhalli da suke zama ’yan gudun hijira da tabarbarewar harkokin rayuwa da tsaro a yankin zuwa wasunsu.
An dauki wasu matakai don a ceto tafkin a 1994, lokacin aka gano cewa sako ruwa daga kogin Ubangi da ke Afirka ta Tsakiya zuwa Tafkin Chadi zai taimaka wajen farfado da shi, aiki da zai ci Dalar Amurka miliyan shida.
Taron shugabannin kasashen gabar tafkin (LCBC) a shekarar 2002 da aka gudanar a Jammaina na kasar Chadi ya amince da shirin zuba jari na shekara biyar domin inganta jawo ruwa daga Kogin Chari zuwa tafkin da bunkasa Tafkin Chadi tare da gudanar nazari kan yadda za a samar da cudanya a tsakanin ruwan da ke kasa da kuma kogunan da dan Adam ya kirkira.
Shirin ya fara gudana a matakin farko kafin shirin janyo ruwan, kuma ana sa ran ya bude hanya da samar da yanayi mai kyau na aiwatar da shirin jawo ruwa daga Kogin Ubangi a kan Dala miliyan 14.
Bankin Bunkasa Afirka da Bankin Bunkasa kasashe na Musulunci sun nuna sha’awar shiga cikin shirin a lokacin. Sai dai kasashen Hukumar Raya Kogunan Kongo-Ubangi- Sangha da suka hada da Jamhuriyyar Dimokuradiyyar Kongo da Jamhuriyyar Kongo da Afirka ta Tsakiya sun nuna damuwa cewa wannan aiki zai kawo cikas ga aikin samar da wutar lantarki na Madatsar Inga kuma ya yi illa ga kogunan Ubangi da Kongo sannan ya rage yawan kifin da suke samu. Babu mamaki wannan martani ya kawo nakasu ga daukacin wannan shiri, kuma ya yi kusan kashe shi gaba daya.
Sai dai duk da haka sakamakon sake farfado da shirin a yanzu inda Najeriya ta sake Dala miliyan biyar don nazarin yadda aikin zai gudana, bayanin Buhari kan shirin zai kara karfafa yunkurin da ake yin a ceto Tafkin Chadi a lokacin da yah au gadon mulki.
kasashen yankin wajibi ne su kawar da mugun tunanin da suke nunawa a baya kan shirin su fito su nuna da gaske suke yi wajen sake farfado da tafkin kamar yadda yake a baya, harkokin tattalin arzikin da ke cikin hakan suna da yawa, kuma za a samu ninki ba ninki marar iyaka ga daukacin yankin.