Chadi ta rufe iyakokinta da Jamhuriyar Tsakiyar Afrika

Shugaban kasar Chadi Idriss Deby ya umarci rufe kan iyakokin kasar da Jamhuriyar Tsakiyar Afrika har sai kasar ta kawo karshen rikicin kabilanci da na addini wanda ya yi sanadiyyar mutuwar dubbannin mutane da kuma tilasta wa wasu miliyoyi kaurace wa muhallinsu.  Shugaban ya bayyana matakin ne ranar Lahadin da ta gabata a lokacin da […]

Chadi ta rufe iyakokinta da Jamhuriyar Tsakiyar Afrika
Chadi ta rufe iyakokinta da Jamhuriyar Tsakiyar Afrika

Shugaban Kasar Chadi Idriss DebyShugaban kasar Chadi Idriss Deby ya umarci rufe kan iyakokin kasar da Jamhuriyar Tsakiyar Afrika har sai kasar ta kawo karshen rikicin kabilanci da na addini wanda ya yi sanadiyyar mutuwar dubbannin mutane da kuma tilasta wa wasu miliyoyi kaurace wa muhallinsu.  
Shugaban ya bayyana matakin ne ranar Lahadin da ta gabata a lokacin da ya kai ziyara garin Daha wanda ke da nisan Kilomita 20 daga iyakar kasar da Jamhuriyar Tsakiyar Afrika. Amma Mista Deby ya ce za a bar iyakar da ta kai fadin Kilomita 1000 a bude domin a ba ’yan kasar da ke Jamhuriyar Tsakiyar Afrikar damar komowa gida.
Aikin samar da zaman lafiya da dakarun kasar Faransa da kuma wasu daga kasashen Afrika suke gudanawar a kasar, ya kasa tsai da rikicin. Fada dai ya barke ne a kasar bayan mayakan Musulmi na kungiyar Seleka sun hanbarar da gwamnatin François Bozizé  a watan Maris din shekarar 2013.  A wani mataki don shawo kan rikicin, an tilasta wa gwamnatin Michel Djotodia wanda yake Musulmi ne, ya sauka daga mulki saboda matsin lanbar da kuma kashe-kashen da kungiyar Kristoci ta anti-Balaka ke wa Musulmi da ke zaune a kasar. Sai dai wasu na zargin Chadi da mara wa ’yan kungiyar Seleka baya.