Chadi ta tura sojoji dubu 2 da 500 zuwa Kamaru

Gwamnatin kasar Chadi ta tura taimakon kayan yaki da sojoji da kuma motoci 400 zuwa kan iyakokin kasar Kamaru da Najeriya domin su karfafa wa dakarun kasar Kamaru gwiwa wajen yakar kungiyar Boko Haram. Shugaban kasar Chadi Idriss Deby, ya raka jerin ayarin motocin dakarun kasar shi zuwa kan iyakar Kamaru da Chadi domin ya […]

Chadi ta tura sojoji dubu 2 da 500 zuwa Kamaru
Chadi ta tura sojoji dubu 2 da 500 zuwa Kamaru

Gwamnatin kasar Chadi ta tura taimakon kayan yaki da sojoji da kuma motoci 400 zuwa kan iyakokin kasar Kamaru da Najeriya domin su karfafa wa dakarun kasar Kamaru gwiwa wajen yakar kungiyar Boko Haram.

Shugaban kasar Chadi Idriss Deby, ya raka jerin ayarin motocin dakarun kasar shi zuwa kan iyakar Kamaru da Chadi domin ya karfafa musu gwiwa wurin sauke sabon nauyin da aka dora musu , wanda shi ne yaki da kungiyar Boko Haram. Bayan haka Shugaban kasar Chadi ya yi kuma kira ga sauran kasashen yankin Afirka ta Tsakiya da su biyo sahu domin jerawa da su wurin yaki da kungiyar.
Hakazalika, lokacin da dakarun suka shiga birnin Kousseri mai iyaka da birnin N’Djamena, jama’a a suma sun yi fitowar dango a gefen tituna suna shewa, suna jinjina ga sojoji suna musu fatan alheri domin samun nasara a duk tsawon tafiyarsu zuwa filin daga. A bayanin da Shugaban kasar ya yi, ya ce sun amsa kiran da Shugaban kasar Kamaru Paul Biya ya yi, hakan ya sa ba za su iya nuna halin rashin damuwa ba game da abin da ya shafi makwabtansu.
Hakan nan ma a kasar Chadi jama’a sun fito da dama, inda suka yi jerin gwano wurin nuna goyon bayansu ga yakin da dakarun Chadi za su fara yi da ta’addanci masamman ma da kungiyar Boko Haram. Firaministan kasar Chadi Kalzeubé Payimi Deubet shi ne ya jagoranci jerin gwanon a birnin N’Djamena.
Sai dai a lokacin da ake cikin raba dakarun na kasar Chadi a wurare daban-daban, kungiyar Boko Haram da sake kai wani hari a wasu garuruwa biyu wato Mabass da kuma Maky na lardin Arewa-mai-Nisa kusa da garin Mokolo. Rahotanni kuma sun tabbatar da cewa maharan sun kone garuruwan baki daya, akalla mutane uku ne suka rasa rayukansu a yayin da aka yi garkuwa da tarin jama’a da aka ce sun fi 80. Wannan adadin na jama’a da aka yi garkuwa da su shi ne mafi yawa daga cikin ire-iren garkuwar da kungiyar Boko Haram ta taba yi a kasar Kamaru.
Sai dai har a yanzu ba a tantance ko mutun guda ba daga cikin wannan adadin. Har ila yau, ba a san inda aka kai su ba, da kuma yadda aka sace mutanen . Kwana guda bayan wannan garkuwar, wasu mutane 24 daga cikin kusan tamanin 80 da aka yi garkuwa da su sun samu kubuta. Wannan ya nuna a karo na farko ke nan bayan wasu sa’o’i daga bisani jami’an tsaro na Kamaru suka samu karbo jama’a a cikin tarihin garkuwar da suka bude babinta a Kamaru. Sai dai kuma duk da haka, akwai wasu rahotannin da suke cewa jama’a na garuruwa biyu da kuma na kewayen inda aka sace jama’a na ci gaba da kauracewa daga matsuguninsu, suna neman mafaka a cikin kasa. Kakakin Gwamnati Issa Tchiroma Bakary ya ce, “har idan ba su kai wa kungiyar Boko Haram hari har cikin mabuyansu ba, za su ci gaba da samun fa’idar abin da da suke yi,” Inji shi.
Har ila yau, a shekaranjiya Laraba ne Gwamnatin kasar Kamaru ta ce ta kwato Bajamushen da kungiyar Boko Haram ta sace a watan Yulin bara. A cewar gwamnatin an kwato Bajamushen ne bayan wani farmaki da dakarunta da na kawayenta suka kai wa ‘yan kungiyar ta Boko Haram. Kafin darkuwa da shi, Bajamushen malamin makaranta ne a kasar.