Chelsea ta dauki Joāo Félix a matsayin aro
Dan wasan zai zauna a matsayin aro har zuwa karshen kakar wasanni ta bana.
Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta dauki dan wasan gaban Atletico Madrid, Joāo Félix, a matsayin aro.
Kungiyoyin biyu sun cimma yarjejeniyar aron dan wasan na tsawon wata shida, kafin daga bisani ya koma kungiyarsa.
- An cafke mutum 2 da AK47 da alburusai 325 a Zamfara
- Jami’an tsaro sun ceto karin fasinjar jirgin kasan Edo
Dan wasan ya ce, “Na yi farin cikin zuwa Chelsea saboda babbar kungiya ce; Ina fatan zai taimaka mata wajen cika burinta.”
Joāo Félix dai ya sha suka kan niyyarsa ta barin Atletico Madrid.
Amma kungiyar ta cimma yarjejeniyar sake ba shi dama tare da sake yi masa tayin sabon kwantaragi zuwa 2027.
Dan wasan zai tafi Landan a ranar Laraba tare da iyalinsa don yi masa gwajin lafiya.
Chelsea za ta dauki nauyin albashinsa na tsawon lokacin da zai zauna da kungiyar.
Kazalika, za ta biya Yuro miliyan 11 kudin daukar aronsa daga Atletico Madrid.
Chelsea dai na ci gaba sa yi wa kanta garambawul sakamakon rashin nasara da take fama da shi.
A baya-bayan nan ta yi rashin nasara a hannun Manchester City sau biyu cikin kwana hudu, inda aka lallasa ta da ci biyar da babu.