Chelsea ta dauko hanyar hana Kante barin kungiyar
Kante ya ki tsawaita kwantaraginsa a Chelsea saboda koma bayan da take fuskanta a yanzu.
Wasu bayanai na nuna cewa, kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta soma daukar matakin hana dan wasanta na tsakiya, Ngolo Kante raba gari da ita.
Kawo Mauricio Pochettino Chelsea ne kadai zai kange shirin Ngolo Kante daga raba gari da kungiyar wadda ke fuskantar gagarumin koma baya.
- Aisha Buhari da matar Tinubu sun yi ran gadin Fadar Shugaban Kasa
- An gurfanar da tsohon fira ministan Pakistan kan zargin rashawa
Kante mai shekaru 32 har zuwa yanzu yaki amincewa da sanya hannu kan yarjejeniyar tsawaita kwantiraginsa wanda ake alakantawa da halin da kungiyar ke ciki.
Sai dai Chelsea na ganin kawo Pochettino zai bai wa dan wasan na Faransa kwarin gwiwar ci gaba da zama.
A cewar Chelsea sai da ta tattauna da Kante gabanin raba gari da manajojinta 2 da ta kora a baya-bayan nan.
Yanzu haka dai ana tattaunawa tsakanin Pochettino da Chelsea kuma akwai yiwuwar cimma jituwa cikin makon nan.
Akwai dai alaka mai karfi tsakanin Pochettino da Kante wanda a wancan lokacin ya so daukar dan wasan na tsakiya zuwa PSG a Faransa.
Ngolo Kante wanda ya lashe kofin duniya da Faransa a 2018, ana ganin zai iya ci gaba da zama a Stamford Bridge idan har ragamar horarwar ta koma hannun Pochettino.