Chelsea ta doke Brighton, Palmer ya kafa sabon tarihi 

Palmer ya kafa sabon tarihin zama ɗan wasa na farko a gasar Firimiyar Ingila da ya taɓa jefa ƙwallo huɗu a raga kafin hutun rabin lokaci.

Chelsea ta doke Brighton, Palmer ya kafa sabon tarihi 

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea ta doke Brighton Hove & Albion da ci 4 da 2 a gasar Firimiyar Ingila.

Ɗan wasan tsakiyar Chelsea, Cole Palmer ya kafa sabon tarihin zama ɗan wasa na farko a gasar Firimiyar Ingila da ya taɓa jefa ƙwallo huɗu a raga kafin hutun rabin lokaci.

Yanzu haka dai Chelsea na mataki na huɗu a gasar da maki 13 daga wasanni shida da buga a kakar wasanni ta bana.

Palmer ya jega ƙwallo a minti na 21 da 28 da 31 da 41.

Ita kuwa ƙungiyar Brighton ta jefa ƙwallayenta a minti na 7 da minti na 34, daga hannun ’yan wasanta Rutter da Carlos Baleba.

Cole Palmer, wanda ɗan asalin Ingila ne, ya jefa wa Chelsea ƙwallo 31, yayin da ya taimaka aka zura ƙwallo 19 a raga daga wasanni 52 ya buga wa ƙungiyar.

Palmer ya koma Chelsea ne daga Manchester City kan kuɗi Yuro miliyan 40 a kakar da ta wuce.

Sojoji sun lalata sansanin Bello Turji, sun kuɓutar da mutum 7

Wani mutum ya rasu yayin gyaran rijiya a Kano

Matashi ya shiga hannu kan safarar tabar wiwi

Na yi shekara 20 ina fim amma har yanzu ina fama da talauci — Djimon Hounsou