Chelsea ta fara Gasar Firimiyar bana da rashin sa’a 

Chelsea ta yi cafane don tunkarar karar wasanni ta bana.

Chelsea ta fara Gasar Firimiyar bana da rashin sa’a 

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea, ta sha kashi da ci 2 da nema a hannun Manchester City.

Chelsea ta karɓi baƙuncin Manchester City a gidanta, da yammacin ranar Lahadi.

Sai dai ƙungiyar ta gaza doke City a gaban magoya bayanta.

Erling Haaland ne, ya fara jefa wa Manchester City ƙwallo a raga a minti na 18 da fara wasa.

Sai kuma tsohon ɗan wasan tsakiyar Chelsea, Mateo Kovacic, ya jefa ƙwallo ta biyu a minti na 85.

Ɗan wasan gaban Chelsea, Nikolas Jackson, ya jefa mata ƙwallo a minti na 44, amma na’urar VAR ta kashe ƙwallon, inda ta ce ɗan wasan ya yi satar fage.

Chelsea dai ta sake kashe maƙudan kuɗaɗe wajen yin cefane, ciki har da sauya mai horaswa domin tunkarar kakar wasanni ta bana.

Sai dai ya zuwa yanzu a iya cewa ba a san ma ci tuwa ba, sai miya ta ƙare.