Chelsea ta fara yunkurin korar Jose Mourinho
Alamu sun nuna kulob din Chelsea na Ingila ya fara tunanin korar kocinsa Jose Mourinho muddin bai farfado da kulob din a kakar wasa ta bana ba. A ranar Lahadin da ta wuce ne kulob din Manchester City ya lallasa na Chelsea da ci 3-0 sakamakon da ya ba magoya bayan kulob din matukar mamaki […]
Alamu sun nuna kulob din Chelsea na Ingila ya fara tunanin korar kocinsa Jose Mourinho muddin bai farfado da kulob din a kakar wasa ta bana ba. A ranar Lahadin da ta wuce ne kulob din Manchester City ya lallasa na Chelsea da ci 3-0 sakamakon da ya ba magoya bayan kulob din matukar mamaki da kuma takaici.
Kawo yanzu kulob din Chelsea ya hada maki 1 ne kacal daga cikin wasanni biyu da ya yi a gasar rukunin firimiya na Ingila. Wani rahoto da kafafen watsa labarai suka kalato daga kulob din sun nuna kocin ya dauki wadansu matakai da ba su yi wa mahukunta kulob din dadi ba. A wasan farko ne aka ruwaito kocin ya zargi Likitar da ke kula da ’yan wasan akan yadda ta yi wa dan kwallonsu Eden Hazard allurar da ya kashe maza kuzari a wasan da kulob din ya yi da na Stoke City inda aka tashi wasan da ci 2-2. A wasa na biyu da Man City kuma sai kocin ya canza dan kwallon bayansa John Terry da gangan inda ya maye gurbinsa da dan kwallon gaba Cuadrado, al’amarin da ya ba magoya bayan kulob din mamaki. Sai dai wasu sun yi hasashe kocin ya yi haka ne don ya janyo hankalin mai kulob din Abrahamobic akan akwai bukatar ya sayo dan kwallon baya kafin a rufe kakar saye da kuma sayar da ’yan kwallo.
Sannan abin takaici ne ganin kulob din ne yake rike da kofin firimiya a yanzu amma tun ba a je ko’ina ba ya fara yin tangal-tangal. Wadannan da ma wadansu dalilai ta sa kulob din ya fara tunanin raba-gari da kocin.
Idan za a tuna wannan shi ne karo na biyu da kocin yake horar da kulob din. Kocin ya taba horar wa a kulob din Inter Milan na Italiya da na Real Madrid da ke Sifen kafin ya sake komawa kulob din Chelsea na Ingila a karo na biyu.