Chelsea ta kori Jose Mourinho
A jiya Alhamis ne kulob din Chelsea ya bayar da sanarwar korar kocinsa Jose Mounrinho wata bakwai bayan ya taimaka wa kulob din lashe gasar firimiya ta Ingila da kuma kofin Kalin (Carling Cup) a kakar wasan da ta wuce.Mourinho dan shekara 52, a watan Yunin 2013 ne ya sake zama kocin Chelsea a karo […]

A jiya Alhamis ne kulob din Chelsea ya bayar da sanarwar korar kocinsa Jose Mounrinho wata bakwai bayan ya taimaka wa kulob din lashe gasar firimiya ta Ingila da kuma kofin Kalin (Carling Cup) a kakar wasan da ta wuce.
Mourinho dan shekara 52, a watan Yunin 2013 ne ya sake zama kocin Chelsea a karo na biyu bayan ya bar kulob din a karo na farko a shekarun baya inda ya koma kulob din Inter Milan na Italiya daga nan ya koma na Real Madrid da ke Sifen kafin daga baya ya sake komawa kulob din Chelsea a shekarar 2013.
A bara ne dai Chelsea ta lashe gasar firimiya da tazarar maki takwas sai dai a bana kulob din ya shiga cikin mawuyacin hali. Kawo yanzu kulob din ne na 16 a teburin gasar firimiya bayan an lallasa shi a wasanni 9 daga cikin wasanni 16. A ranar Litinin ce kulob din Leicester City ta lallasa na Chelsea da ci 2-1 a gasar rukunin firimiya al’amarin da ya harzuka mai kulob din Roman Abramobich da wasu daga cikin magoya bayan kulob din al’amarin da ya sa ya dauki matakin sallamarsa.
Rahotanni sun nuna tuni kulob din ya fara zawarcin kocin da zai maye gurbin Mourinho. An ce kulob din ya fara karkata akalarsa ne a kan Pep Guardiola ko Guus Hiddink ko Brenden Rodgers ko kuma Juande Ramos. A cikin wadannan kococi ne ake ganin daya daga cikinsu zai iya maye gurbin Mourinho.
Tun a watan jiya ne dai aka rika rade-radin kulob din Chelsea zai yi hannun riga da Mourinho, sai dai wadansu masana harkar kwallo ciki har da tsohon kocin Manchester United sun tausayawa Mourinho inda suka nuna a kara masa lokaci watakila ya farfado da martabar kulob din amma yanzu ta faru ta kare tun da kulob din ya dauki matakin sallamarsa.