Chelsea ta kulla yarjejeniya da FC Barcelona a kan Fabregas
Rahotanni da ke fitowa daga Sifen sun tabbatar kulob din Chelsea da ke Ingila ya kulla yarjejeniya da kulob din FC Barcelona na Sifen a kan dan kwallonta Cesc Fabregas.Kamar yadda jaridar da ake wallafawa a Sifen mai suna Mundo Deportibo ta nuna, kulob din Chelsea ya yi shigar sauri don dauke dan kwallo Fagbregas […]

Rahotanni da ke fitowa daga Sifen sun tabbatar kulob din Chelsea da ke Ingila ya kulla yarjejeniya da kulob din FC Barcelona na Sifen a kan dan kwallonta Cesc Fabregas.
Kamar yadda jaridar da ake wallafawa a Sifen mai suna Mundo Deportibo ta nuna, kulob din Chelsea ya yi shigar sauri don dauke dan kwallo Fagbregas ne bayan kulob din ya yi ban kwana da dan kwallon tsakiyarsa Frank Lampard. A ranar Litinin da ta wuce ne Lampard ya tabbatar wa duniya cewa ya bar kulob din Chelsea bayan kwantaraginsa ta kare a kulob din.
Rahoton ya nuna FC Barcelona na neman Chesea ta ajiye mata zunzurutun Fam miliyan 29.2 akan dan kwallon kafin ta amince ya koma Ingila, sai dai ya juya shekaranjiya Laraba tattaunawa a tsakanin kulob din biyu ta yi nisa don cimma matsaya a kan batun dan kwallon.
Kulob din Manchester United da na Manchester City da kuma na Arsenal dukkaninsu a Ingila suna daga cikin wadanda ke zawarcin Fabregas kafin a fara kakar wasa mai zuwa.