Chelsea ta lashe gasar Fifa Club World Cup
Karon farko ke nan a tarihi da Chelsea ta lashe gasar.
Chelsea ta lashe gasar FIFA Club World Cup
Chelsea ce kungiyar kwallon kafa da ta zama gwarzuwar duniya bayan ta lashe gasar cin kofin kungiyoyin kasashen duniya ta Fifa Club World Cup a daren ranar Asabar ta gabata.
Karon farko ke nan a tarihi da Chelsea ta lashe gasar bayan ta samu nasarar doke kungiyar Palmeiras ta kasar Brazil da ci 2-1.
- Jami’an tsaro sun kwato mutane 3, sun kashe dan bindiga a Kaduna
- 2023: Lokaci ya yi da ’yan Arewa za su yi wa Tinubu sakayya —Shettima
A minti na 117 ne dai dan wasa Kai Havertz ya zura kwallon da ta bai wa Chelsea nasara, bayan kungiyarsa ta samu bugun daga kai sai mai tsaron raga a fafatawar da ta gudana a birnin Abu Dhabi da ke Hadaddiyar Daular Larabawa.
Ko a gasar cin Kofin Xakarun Turai na shekarar 2021 dan wasa Kai Havertz ne ya zura kwallon da kungiyarsa ta Chelsea ta yi nasara a kan Manchester City da ci daya mai ban haushi.

Wannan nasarar da Chelsea tayi ya sa ta lashe ko wacce gasa a duniya karkashin jagorancin Shugaban Kungiyar, Roman Abramovich.
Tun da fari dai dan wasa Romelu Lukaku ya fara zura kwallon farko a minti na 54, kafin dan wasa Raphael Veiga ya farke ta a minti na 64, lamarin da ya kai ga an buga minti 90 da sakamakon kunnen doke.
A kan haka ne wasan ya gai ga karin minti 30, inda ana sauran minti 3 a tashi wasan kuma ya kai ga bugun fenareti, Chelsea ta samu nasarar kara kwallo daya.
Bayanai sun ce a kasar Japan aka shirya buga gasar FIFA Club World Cup ta bana, sai dai a watan da ya gabata aka sauya shawara a sakamakon karuwar adadin mutanen da cutar Coronavirus ta harba a kasar.
Ana dai gudanar da wannan gasa ce a tsakanin kungiyoyin da suka zama zakara a gasar nahiyoyi daban daban da ke fadin duniya, hadi da kungiyar da lashe gasar kasar da za ta yi wa gasar masaukin baki.