Chelsea ta naɗa Maresca a matsayin sabon kocinta
Maresca ya zama kocin Chelsea na shida bayan da aka yi wa ƙungiyar garambawul.
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea ta ɗauki kocin Leicester City, Enzo Maresca a matsayin sabon kocinta bayan raba gari da Mauricio Pochettino.
Kocin mai shekara 44 ɗan asalin ƙasar Italiya, ya je Leicester City a 2023, inda ya jagorance su wajen dawowa gasar Firimiyar Ingila.
- Ban taɓa tsammanin zan kai wata guda a matsayin gwamna ba — Fubara
- HOTUNA: Yadda yajin aikin NLC ya tsayar da harkoki a Najeriya
“Muna farin cikin yi wa Enzo Maresca barka zuwa wannan ƙungiya,” cewar Chelsea.
Maresca ya rattaba hannun shekara biyar a Chelsea, kuma zai fara aiki gadan-gadan a ranar 1 ga watan Yuli, 2024.
Pochettino ya raba gari da Chelsea a watan da ya wuce, bayan yarjejeniyar da suka yi na yin rabuwar arziƙi.
Maresca zai zama kocin Chelsea na shida, tun bayan da Todd Boehly ya karbi shugabancin ƙungiyar shekara biyu da ta wuce.
Chelsea ta kashe zunzurutun kuɗi sama da dala biliyan ɗaga wajen yi wa ƙungiyar garambawul, bayan da Roman Abramovich ya sayar da ƙungiyar a 2022.