Chelsea ta sayi dan kwallon Senegal
A ranar Talatar da ta wuce ne kulob din Chelsea na Ingila ya bayar da sanarwar saye dan kwallon baya na Senegal Papy Djilobodji da yake buga wa kulob din FC Nantes na Faransa kwallo.Sayen dan kwallon ya kawo karshen zawarcin da kulob din Chelsea yake yi wa dan kwallon baya a kulob din Eberton […]
A ranar Talatar da ta wuce ne kulob din Chelsea na Ingila ya bayar da sanarwar saye dan kwallon baya na Senegal Papy Djilobodji da yake buga wa kulob din FC Nantes na Faransa kwallo.
Sayen dan kwallon ya kawo karshen zawarcin da kulob din Chelsea yake yi wa dan kwallon baya a kulob din Eberton na Ingila John Stone. Kulob din ya ce sun kulla yarjejeniyar ce da dan kwallo Papy na tsawon shekara hudu.
“Kulob dub FC Nantes da ke Faransa ya cimma matsaya da na Chelsea da ke Ingila a kan dan kwallon baya Papy Djilobodji akan kwantaragin shekara hudu”, a wata sanarwa da kulob din ya fitar ranar Talatar da ta wuce.
Papy Djilobodji dai yana buga kwallo ne a bangaren baya (defender) kuma yana daga cikin ’yan kwallon da ke yi wa Senegal kwallo a halin yanzu.