Chelsea za ta sabunta kwantaragin Jose Mourinho
Kulob din Chelsea da ke Ingila ya fara yunkurin tattaunawa da kocinsa Jose Mourinho don ganin ya sabunta kwantaraginsa. A da kwantaragin kocin za ta kare ne a shekarar 2017 don haka kulob din yake son kara wa kocin wa’adin shekara biyu zuwa shekarar 2019. Kulob din ya yanke shawarar kara wa kocin wa’adi ne […]
Kulob din Chelsea da ke Ingila ya fara yunkurin tattaunawa da kocinsa Jose Mourinho don ganin ya sabunta kwantaraginsa. A da kwantaragin kocin za ta kare ne a shekarar 2017 don haka kulob din yake son kara wa kocin wa’adin shekara biyu zuwa shekarar 2019.
Kulob din ya yanke shawarar kara wa kocin wa’adi ne bayan ya samu nasarar lashe gasar rukunin firimiya na Ingila a bana bayan ya shafe kimanin shekara biyar ba tare da lashe kofin. Sannan kocin ya samun nasarar lashe kofin Carling na Ingila a bana. Wannan nasarori da kocin ya samu ne ta janyo hankalin kulob din wajen sabunnta kwantaragin kocin.
Rahotonni sun ce a yanzu kocin yana karbar albashin da ya kai Fam miliyan 12 da rabi kwatankwacin Naira Biliyan 4 da miliyan 262 da dubu 500 a shekara a kulob din na Chelsea tsohon amma ana kyautata zaton zai samu kari a kan sabon kwantaragin.
Kocin ya koma bakin aiki ne a shekaranjiya Laraba, bayan ya samu hutu jim kadan bayan ya lashe gasar firimiya ta Ingila a ranar Lahadi da ta wuce. Wannan shi ne karo na uku da kocin yake lashe wa kulob din kofin firimiya na Ingila baya ga wasu kofuna.