Chelsea za ta yi musayar Victor Moses da kulob din Everton

Da alama dan kwallon Najeriya da ke kwallo a kulob din Chelsea Victor Moses ya kama hanyar barin kulob din zuwa na Everton a wani musaya da kulob din biyu suke niyyar yi, kamar yadda wani rahoto da ke fitowa daga kulob din ya nuna a shekaranjiya Laraba.Rahoton ya nuna cewa kulob din Chelsea ya […]

Chelsea za ta yi musayar Victor Moses da kulob din Everton
Chelsea za ta yi musayar Victor Moses da kulob din Everton

Da alama dan kwallon Najeriya da ke kwallo a kulob din Chelsea Victor Moses ya kama hanyar barin kulob din zuwa na Everton a wani musaya da kulob din biyu suke niyyar yi, kamar yadda wani rahoto da ke fitowa daga kulob din ya nuna a shekaranjiya Laraba.
Rahoton ya nuna cewa kulob din Chelsea ya fara yunkurin yin musaya ne da Victor Moses da kuma dan kwallon baya a kulob din Everton mai suna John Stones.
Rahoton ya ce tuni kulob din na Chelsea ya taya John Stones akan Fam miliyan 20, dan kwallon da suke ganin shi zai maye gurbin dan kwallon bayansu John Terry.
Sai dai Everton ta ki amincewa da tayin Fam miliyan 20, hasalima kulob din ya nuna sai Chelsea ta ajiye masa akalla Fam miliyan 30 ne kafin ta bar John Stones ya canza sheka.  Akan haka ne Chelsea take tunanin hada kudi da dan kwallonta Victor Moses a cinikin don ganin ta shawo kan Everton.
Victor Moses dai yay i wa kulob din Stoke City wasa ne a kakar was an da ta wuce a matsayin aro.  Duk kokarin da yay i na kulob din ya saye shin a dindindin abin ya ci tura al’amarin da ya sake mayar da shi kulob din Chelsea a kakar wasa ta bana.

’Yan sanda sun kashe ’yan fashi 3 a Binuwai

Mahara sun sace bsarake, sun harbi matarsa a ƙauyen Ondo

Sarkin Musulmi ya umarci a fara neman jinjirin watan Muharram

An tsinci gawar wata mata babu kai a Abuja