Chibok: Amurka ta turo sojojinta Najeriya … Faransa da Birtaniya da China ma za su turo
kasar Amurka ta turo wata tawaga da ta kunshi kwararru a kan tsaro zuwa kasar nan, wadanda za su taimaka wajen neman ’yan matan Chibok da ’yan Boko Haram suka sace fiye da mako uku da suka gabata.A hirar da ya yi da wata kafar talabijin a Amurka, Shugaban Amurka Barack Obama ya ce tawagar […]

kasar Amurka ta turo wata tawaga da ta kunshi kwararru a kan tsaro zuwa kasar nan, wadanda za su taimaka wajen neman ’yan matan Chibok da ’yan Boko Haram suka sace fiye da mako uku da suka gabata.
A hirar da ya yi da wata kafar talabijin a Amurka, Shugaban Amurka Barack Obama ya ce tawagar ta kunshi sojoji da jami’an tsaro da kuma jami’an wasu hukomomi da za su yi kokarin gano takamaiman wurin da aka ajiye ’yan matan.
Shugaba Obama ya bayyana ’yan matan da’yan Boko Haram suka sace, a matsayin abin tausayi da kuma takaici, inda ya yi tir da lamarin. Ya ce watakila lamarin ya sa kasashen duniya su farga wajen yin aiki tare, domin daukar mataki a kan kungiyar Boko Haram.
Jami’an Amurka sun ce watakila an wuce da wasu daga cikin ’yan mata zuwa kasashen Chadi da Kamaru da ke makwabtaka da Najeriya kodayake jami’ai a kasashen Chadi da Kamaru sun musanta haka.
A wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, Sakataren Harkokin Wajen Amurka John Kerry ya ce Shugaban Goodluck Jonathan ya bude hannu domin amsar tayin taimako da Amurka ta yi masa ta wayar tarho a tattaunawar da ya yi da Jonathan din.
“Ofishin jakandancinmu a Abuja a shirye yake ya hada kan kwararru da za su ba da gudunmawar kwarewa a kan harkokin tattara bayanai da bincike da karbar mutanen da aka yi garkuwa da su,” inji Ma’aikatar Harkokin Waejn Amurka.
Kakakin Ma’aikatar Jen Psaki ta ce daga cikin agajin da Amurka za ta ba Najeriya har da sojoji da ’yan sanda.
Mai ba Shugaban kasa shawara kan labarai Reuben Abati, ya ce Shugaba Jonathan ya gana da manyan hafsoshin tsaron kasa bayan ganawa da Kerry.
kasar Faransa ma ta bayyana niyyarta ta taimaka wa Najeriya da sojoji da kwararru, domin nemo ’yan matan Chibok din.
Ministan Harkokin Wajen Faransa, Laurent Fabius ya ce Shugaba Francois Hollande ya umarce shi ya shaida wa Shugaban Najeriya cewa, kasar za ta iya amfani da sojoji da kayan yakin Faransa da ke yankin, domin ceto ’yan matan.
Fabius ya shaida wa majalisar dokokin kasar a shekaranjiya Laraba cewa, ganin girman yanayin da ake ciki dole Faransa ta dauki mataki.
Ita ma Birtaniya za ta turo da karamar tawagar kwararru kan sha’anin tsaro zuwa kasar nan, domin nemo ’yan matan.
Sai dai Birtaniya ta ce kwararrun ba za su shiga cikn daji da kansu, domin gano inda aka boye daliban matan ba.
kasar China ma ta mika tayin taimako ga Najeriya, ta hanyar horar da dakarunta a fagen yaki da ta’addanci.
Wata sanarwa daga fadar Shugaba Jonathan ta ce Najeriya ta amince da tayin taimakon Birtaniyar da China.