Chibok: Rundunar ’yan sanda za ta ba da ladar Naira miliyan 50
Rundunar ’Yan sandan Najeriya ta ba da sanarwar ba da tukuicin Naira miliyan 50 ga duk wanda ya taimaka da bayanan da za su kai ga ganowa da kuma ceto ’yan mata dalibai da aka sace daga makarantar sakandare ta Chibok da ke Jihar Borno. Wata sanarwa da ta fito daga hedkwatar ’yan sandan ta […]
Rundunar ’Yan sandan Najeriya ta ba da sanarwar ba da tukuicin Naira miliyan 50 ga duk wanda ya taimaka da bayanan da za su kai ga ganowa da kuma ceto ’yan mata dalibai da aka sace daga makarantar sakandare ta Chibok da ke Jihar Borno.
Wata sanarwa da ta fito daga hedkwatar ’yan sandan ta kasa da ke Abuja, dauke da sanya hannun Kakakin Rundunar CSP Frank Mba ta ce duk wanda ya ba da bayanai, za a yi amfani da bayanan a cikin sirri ba tare da al’umma sun sani ba.
Sanarwar ta kuma bukaci jama’ar kasar nan da suke da bayanai game da lamarin su tuntubi ’yan sanda a wasu lambobin wayoyin salula guda shida da suka hada da: 09-2914649 da 08081777309 da 08055547536 da 08032125050 da 08034617591 da kuma 08035969731.
Rundunar ’yan sanda ta kuma bukaci al’ummar kasar nan su taimaka waje shawo kan kalubalen tsaron da ake fama da shi a kasar.
A ranar 14 ga watan Afrilu ne ’yan Boko Haram suka sace dalibai ’yan mata 276 a makarantar sakandare ta Chibok da ke Jihar Borno.
Bayan kwana biyu da aukuwar lamarin, Gwamnan Jihar Borno Alhaji Kashim Shettima ya yi tayin ba da ladan Naira miliyan 50 ga duk wanda ya taimaka aka gano inda ’yan matan suke, amma har zuwa hada wannan rahoto ba a samu bayanin inda aka shiga da su ba.