Chile ta lashe kofin Copa Amerika bayan shekara 99
A karon farko tun bayan shekara 99 da fara gasar cin kofin Copa America da ke Kudancin Amurka, kasar Chile ta samu nasarar lashe kofin bayan ta samu nasara a kan Ajantina a wasan karshe a ranar Asabar da ta wuce. Chile ta samu nasarar ce bayan ta samun nasara a bugun fanariti da ci […]
A karon farko tun bayan shekara 99 da fara gasar cin kofin Copa America da ke Kudancin Amurka, kasar Chile ta samu nasarar lashe kofin bayan ta samu nasara a kan Ajantina a wasan karshe a ranar Asabar da ta wuce.
Chile ta samu nasarar ce bayan ta samun nasara a bugun fanariti da ci 4-1 bayan an tashi wasan babu ci watau 0-0 sannan aka sake kara mintuna 30 amma duk da haka wasan bai kaya ba sai a bugun fanariti..
dan kwallon kulob din Arsenal, Aledis Sanchez ne ya zura kwallo ta hudu a bugun na fanariti da hakan ta sa kasarsa ta lashe kofin.
Jim kadan bayan ya zura kwallo a raga ne sai filin wasa mai suna Estadio Nacional Santiago ya barke da murnar dubunan magoya bayan kasar da suka yi cincirindo don mara wa kasarsu baya.
Wannan rashin nasara da Ajantina ta samu, ya sanya shahararren dan kwallon duniya Lionel Messi ya kasa lashe manyan kofuna ga kasar haihuwarsa. A gasar cin kofin duniya da ta gudana a bara, Jamus ce ta doke Ajantina a wasan karshe. Kenan duk da nasarar da Messi ya samu na lashe manyan kofuna uku a kulob din FC Barcelona da ke Sifen a kakar wasan da ta wuce, bai samu nasarar lashe wani kofi da kungiyar kwallon kafa ta Ajantina ba.
Gasar Copa America dai ta hada kasashe 12 ne inda suka fafata da juna. Kuma Chile ce ta dauki nauyin gasar a wannan karo, kuma ga shi ta samu nasarar lashe kofin.
Rabon da Ajantina ta lashe kofin tun a shekarar 1993 watau kimanin shekaru 22 da suka gabata. Chile dai tana da mutanen da aka kiyasta sun kai Miliyan 17.