China ma za ta haramta amfani da mota mai aiki da fetur
kasar China wadda ta fi cinikin motoci a duniya, na shirin haramta kerawa da kuma sayar da motocin da suke amfani da man fetur ko dizal. Mataimakin Ministan Masana’antu na kasar din Guobin ya ce, tuni suka fara nazari a tsanake, sai dai har yanzu ba su yanke shawarar lokacin da za a tabbatar da […]

kasar China wadda ta fi cinikin motoci a duniya, na shirin haramta kerawa da kuma sayar da motocin da suke amfani da man fetur ko dizal.
Mataimakin Ministan Masana’antu na kasar din Guobin ya ce, tuni suka fara nazari a tsanake, sai dai har yanzu ba su yanke shawarar lokacin da za a tabbatar da haramtawar ba.
din Guobin ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na kasar cewa, “Wadannan matakai za su kawo sauyi wajen bunkasa kamfanonin motocinmu.”
Gidan rediyon BBC, ya ruwaiti cewa, China ta kera motoci miliyan 28 a bara, kusan kashi uku na motocin da aka kera a duniya.
Tuni kasashen Birtaniya da Faransa suka sanar da shirin haramta amfani da motoci masu amfani da fetur da dizal a shekarar 2040, a kokarinsu na rage gurbatacciyar iska.
A watan Yuli ne kamfanin kera motoci na bolbo ya ce, daga shekarar 2019 duk sababbin motocin da zai kera za su kasance masu amfani ne da lantarki.
Mai kamfanin bolbo, Mista Geely, ya ce a shekarar 2025 ne yake burin sayar da motoci masu amfani da wutar lantarki har miliyan daya.
Wasu kamfanonin motoci da suka hada da Renault-Nissan da Ford da kuma General Motors dukansu suna aikin samar da motoci masu aiki da wutar lantarki a China.
Kamfanonin kera motocin sun fara fafutikar yadda za su bunkasa kasuwar kasar, wajen gabatar da sababbin dokokin da za su yi yaki da gurbatacciyar iska.
kudirin na bukatar kashi takwas cikin 100 na masu kera motocin sayarwa su zamo baturansu na lantarki ne ko wanda za a hada da wata motar zuwa bada, inda zai karu da kashi 12 cikin 100 a shekarar 2020.
din ya yi hasashen cewa sauyin zai kawo ce-ce-kuce a masana’antar.
Har ila yau hakan zai kawo karshen yawan bukatar man fetur a kasar, inda a yanzu kasar ce ta biyu a duniya da take sayen man fetur bayan Amurka.