China ta gina hanyar da bam ba ya fasawa
kasar China ta shinfida kwalta, wadda bam ba zai iya fasata ba, a kan wata babbar hanya da ke isa Dandalin Tiananmen Skuare da ke birnin Beijing, kamar yadda jaridar kasar mai suna Shenzhen Ebening Post ta wallafa. kasar ta gudanar da aikin ne gabanin wani babban faretin sojin da za a yi a dandalin […]
kasar China ta shinfida kwalta, wadda bam ba zai iya fasata ba, a kan wata babbar hanya da ke isa Dandalin Tiananmen Skuare da ke birnin Beijing, kamar yadda jaridar kasar mai suna Shenzhen Ebening Post ta wallafa.
kasar ta gudanar da aikin ne gabanin wani babban faretin sojin da za a yi a dandalin a watan Satumbar bana.
An shinfida wani abu a karkashin kwaltar, hakan ya sanya kwaltar ta kara kauri da kusan mita guda. Har ila yau, an dasa abubuwan da suke samar da rigakafi daga fashewar bam ciki har da kankare. Kuma a yanzu kaurin kwaltar titin ta nunka ta titunan da aka saba gani har sau biyu.
Wani jami’in gwamnatin kasar ya bayyana cewa ginin hanya yana daya daga cikin manyan ayyukan da ake ci gaba da yi gabanin ranar bikin cika shekara 70 da kawo karshen yakin Duniya na Biyu. Kuma a lokacin bikin ne za a gudanar da wani babban faretin sojoji, wanda shi ne na farko a tarihin kasar da sojojin kasar za su yi tare da takwarorinsu daga wasu kasashen waje.